• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sai Da Ruwan Ciki Ake Jan Na Rijiya

byCGTN Hausa
2 years ago
Rijiya

Sanin kowa ne cewa, babbar matsalar dake addabar wasu sassan duniya a halin yanzu shi ne, batun abinci ko cimaka, sakamakon fadace-fadace, da matsalar fari, ambaliyar ruwa da ta yi awon gaba da amfanin gona ko wasu matsaloli masu nasaba da matsalar sauyin yanayi ko kuma bala’u daga indallahi. Wannan ne ma ya sa, a duk lokacin da aka shirya taruka a lokuta mabambanta ake kira ga kasashen duniya su ba da muhimmanci ga batun samar da abinci, da ma ingantacciyar hanyar warware matsalar ta hanyar hadin gwiwa.

Masana sun sha bayyana cewa, tsarin samar da abinci na duniya “ya tabarbare”, kuma wajibi ne a canza hanyar samar da abinci, da kuma yadda ake amfani da shi, a halin yanzu ta yadda zai dace da ci gaban zamani.

  • An Yabawa Sin Kan Taimakon Ilimi Ga Dalibai Masu Rauni A Habasha 
  • Sin Ta Harba Tauraron Dan Adam Na Gwajin Fasahar Intanet Na Tauraron Dan Adam

Ko da a shawarar da ya gabatar game da raya kasa da kasa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya sanya batun samar da abinci a matsayin daya daga cikin muhimman fannoni guda takwas na hadin gwiwa. Kuma kasar Sin ta gudanar da hadin gwiwa a fannin aikin gona tare da kasashe da yankuna fiye da 140, da inganta fasahohin aikin gona sama da dubu guda ga kasashe masu tasowa, lamarin da ya haifar da karuwar yawan amfanin gona da sama da kashi 30 zuwa 60 cikin 100 a yankunan da suka ci gajiyar wannan tsari.

Bugu da kari, kasar Sin ta horar da dubban kwararru masu sana’ar noman irin shinkafa da aka tagwaita ga kasashe masu tasowa sama da 80, ta kuma gina yankunan gwaji na bunkasa aikin gona, da rage talauci masu tarin yawa, wanda hakan ya taimakawa kasashe masu tasowa, wajen kara kwarewar inganta ayyukan noma da samar da abinci.

Bayanai na nuna cewa, duk da wadannan matakai akwai tarin jama’a a sassan duniya dake fama da yunwa sakamakon wasu matsaloli ko dalilai ko matakan kashin kai da wasu kasashen yamma suka dauka. Matakai da tsare-tsare da kasar Sin ke bijiro da su karkashin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, sun taimaka matuka wajen kara samar da abinci da ma dabarun noma iri-iri a sassan nahiyar.

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Masana na cewa, kasashen Afrika za su iya amfani da huldar dake tsakanin Sin da nahiyar, wajen kawo gagarumin sauyi a tsarin aikin gona, da magance yunwa, da karancin sinadarai masu gina jiki, da kuma habaka tattalin arzikin mazauna yankunan karkara. Uwa uba da matakan magance matsalar sauyin yanayi masu saukin aiwatarwa, wadda shi ne ke haifar da matsalar karancin cimaka.

A yayin da sassa masu ruwa da tsaki a babban taron sauyin yanayi na COP28 a birnin Dubai na hadaddyar daular Larabawa ke fatan tara dalar Amurka biliyan 270 don samar da kudaden tunkarar tasirin yanayi nan da shekarar 2030, wajibi ne shugabanni su dauki matakai tare da cika alkawuran da suka dauka a yayin taron da ma tarukan da suka gabata, don takaita karuwar yanayin zafin duniya zuwa ma’aunin digirin Celcius 1.5, don kare duniyarmu baki daya daga tasirin sauyin yanayi, ta yadda za a kai ga gina duniya mai tsafta da kowa ne bil-Adama zai ji dadin zama a cikinta.

Wannan na kara nuna cewa, idan har ana son wadata kasa da abinci, ya kamata mahukunta su taimakawa manoma da muhimman kayayyakin noma na zamani da ake bukata, ta yadda za su samar da abincin da al’umma ke bukata da ma samun karin kudin shiga, da raya kauyuka, da kuma ci gaba da zamanintar da aikin gona. Sanin kowa ne cewa, abinci shi ne tushen rayuwa. Kamar yadda malam Bahaushe ke cewa, sai da ruwan ciki ake jan na rijiya. Kuma sai ciki ya koshi kafin a iya yin komai na rayuwa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Next Post
Sin Ta Dauki Alhakinta Wajen Tinkarar Sauyin Yanayi

Sin Ta Dauki Alhakinta Wajen Tinkarar Sauyin Yanayi

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version