Gazawar kamfanin NNPCL na cika alkawarin da yayi na fara aikin daya daga cikin matatu hudu na man fetur na kasa da suka zama tamkar yanzu mutum yanzu ba mutum ba, (Matatar Mai ta Fatakwal an ce zata fara aiki bada dadewa ba).Wani abu ne da yake tayar da hankalin al’ummar Nijeriya, musamman ma masu yi wa kasa fatan alhairi.
Idan za a iya tunawa kamfanin NNPCL ya yi ta sa ranar da cewa matatar man za ta fara aiki lokuttan baya amma sai aka kasa cika alkawarin ba kuma tare da wani kwakkwaran dalili ba.Daga watan Disamba na shekarar 2023 zuwa yanzu NNPCL ya bayar da ranaku da dama na fara aikin matatar man da ake sa ran za ta rika tace danyan mai fiye da ganga 210,000 a kullum amma har yanzu babu wata alamar fara yin aikin matatar man.
- Ma’aikatan NNPC Ba Barayi Ba Ne – Mele Kyari
- Mun Gano Hanyoyin Da Ake Satar Man Fetur A Nijeriya – NNPC
A watan jiya ne, shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya sanar da cewa, matatar man za ta fara aiki a farkon watan Agusta. Ga mu muna gab da fita watan Agustan amma har yanzu farkon watan Agustan Kyari bai yi ba kuma har yanzu matatar man na nan bata fara aiki ba.
A watan Maris na shekarar 2021, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayar da kwangilar Dala Biliyan 1.5 ga wani kamfanin kasar Italiya mai suna Tecnimont SPA, domin yi wa matatar man kwaskwarima,an kasa aikin kashi uku da alkawarin kammala shi a cikin wata 18, 24,da kuma 44.An samar da wasu kamfanonin kasar Italiya; Maire Tecnimont da Oil Major Eni a matsayin wadanda za su tallafa wajen gudanar da aikin gaba daya.
Bayan tabbaci a lokutta da dama na fara aikin matatar man, a halin yanzu dole ‘yan Nijeriya za su kara jira na wani lokaci mai tsawo kafiin hakan ta faru. Amma kuma menene dalilin na gazawar NNPCL na bayar da cikakken dalili ga al’ummar Nijeriya a kan ita gazawar cika wancan alkawarin da ta dade tana yi wa al’ummar kasa a kan fara aikin matatar mai ta Fatakwal?
Tabbas, rashin cika alkawarin da aka yi na fara aikin matatar man Fatakwal wani abu ne da ke da alaka da halayyar shugabannin kasar nan, inda shugabanin ke yin alkawari amma sai su ki cikawa, kuma babu wanda zai kama su da wani laifi.A gare su babu wanda ya isa ya kama su da wani laifi, in ba haka ba ai da an kama wani da laifin rashin cika alkawarin tare da hukunta ko wanene shi ko kuma a bayar da kwakkwaran dalilin da ya hana cika alkawarin, musamman ganin alkawurran sun yi yawa.
Amma me zai sa Nijeriya ta damu da rashin aikin matatar man ta Fatakwal da sauran matatun mai na sassan kasar? Wannan na da muhimmanci musamman ma ganin irin makudan kudaden da ake kashewa wajen sayo tataccen man fetur daga kasashen waje.Bayan madudan kudaden da ake tarawa na haraji hakan kuma na dora nauyi a kan naira saboda da kudaden kasashen waje (Dala) ake harkar sayen man fetur daga kasashen waje.
Ministan kudi da tattalin arzikin Nijeriya, Mister Wale Edun, ya bayyana cewa, Nijeriya na kashe fiye da dala miliyan 600 wajen shigo da man fetur a kowane wata.
In har Nijeriya na kashe wadannan kudaden wajen shigo da man fetur to lalle babu dalilin da zai sa NNPCL ta yi wasa wajen tabbatar da matatar man Fatakwal ta fara yin aiki, da sauran matatun man da ake su a sassan kasar Nijeriya.
Akwai tashin hankali matuka duk da dimbin man fetur da kasar nan take da shi amma har yanzu kasar nan ta dogara ne da shigo da man fetur,(ana shigo fiye da kashi 80 na albarkatun man fetur da kasa ke bukata daga kasashen waje).
Gyara tare da yi wa matatar mai ta Fatakwal kwaskwarima wata dama ce da kasar nan za ta rage kudaden da take kashewa wajen shigo da tacaccen man fetur a kan haka dole a hada tare yin duk kokarin da ya kamata na ganin matatar man Fatakwal ta fara aiki ba tare da bata lokaci ba.
Ya kamata mu yi koyi da kasa ta biyu a yawan man fetur a Afirka wato Angola, wadda a halin yanzu ta yi nisa wajen gina karin matatun mai a fadin kasar duk kuwa da tana da matatar mai tace fiye da 65,000 a kullum a garin Luanda.
A halin yanzu Angola na gina sabbin matatun mai guda uku a garuruwan Cabinda, Lobito, da Soyo. Yayin da ake sa ran kaddamar da matatar mai ta Cabinda zuwa karshen wannan shekarar, za a kaddamar da matatun mai na Lobito da Soyo a cikin shekara 2025. Shirin su shi ne kara man da suke tacewa a cikin gida zuwa ganga 400,000 a kowace rana.
Duk da cewa, dokokin kasa sun amincewa samar da matatun mai masu zaman kansu, a halin yanzu matatun masu zaman kansu irin su na Dangote sun fara aiki, bukatar ganin matatun mai na gwamnati sun fara aiki na da muhimmancin gaske. Tabbatar da wadatuwar man fetur a kasa na bukatar sa hannun gwamnati musamman tabbatar da ganin matatun man fetur na kasar mu suna aiki yadda ya kamata.
A kwanan nan ne aka zargi NNPC Limited da bangaren samar da mai da iskar gas na kasa kan yadda ake samun tsadar man fetur da kuma dambarwar da aka yi a kan shirin sayarwa matatar mai ta Dangote danyen mai.
‘Yan Nijeriya na da gaskiya in suka yi tsaye suka nemi da a tabbatar da matatar mai ta Fatakwal ta fara aiki nan take musamman ma ganin ta lamushe fiye da dala biliyan 1.5 tun da aka fara maganar gyara da yi mata kwaskwarima.Ba zai yiwu a ce Nijeriya na kashe dimbin kudade wajen shigo da man fetur amma kuma ana sayar da litar man a kan Naira 1,000, bayan wasu matatun na cikin gida sun yi alkawarin samar da sauki a farashin man ba.
Muna kira ga NNPCL da ta bayyana cikakken halin da matatar man Fatakwal take ciki, domin zuwa yanzu alkawurran da aka dauka na kammala gyaran ana karyawa ya yi yawa, mun kuma gaji haka.