A baya-bayan nan, jagoran ‘yan awaren Taiwan Lai Ching-te, wanda ya kira kansa da “mai rajin neman ‘yancin kan Taiwan”, ya kara ikirarin cewa bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan ba sa karkashin ikon juna, har ma ya ce wai Taiwan wata kasar demokradiyya ce mai mulkin kanta. Amma duk yunkurin Lai Ching-te ba zai iya canza gaskiyar da duniya ta amince da ita ba, wato Taiwan ba ta taba zama kasa ba, kuma ba za ta taba zama ba a nan gaba. Sunan yankin Taiwa a MDD shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”. Manufar Sin daya tak a duniya ra’ayin bai daya ne na al’ummomin duniya, kuma bisa ka’idar ne kasashe 183 suka kulla huldar diflomasiya da Sin.
Ta yaya za a warware batun Taiwan? Tuni dai babban yankin kasar Sin ya tabbatar da cewa, a shirye yake ya yi iyakacin kokari da sahihiyar zuciya domin neman kyakkyawar makomar dinkewar kasar Sin cikin lumana. Amma idan ‘yan aware masu neman “’yancin Taiwan” suka yi tsokana ko tilasta neman ballewa ko ma tabo batu mai tada kura, dole ne zai dauki matakai masu tsauri. Lai Ching-de da mabiyansa da ke wasa da wuta a mashigin tekun Taiwan, za su kone kansu. Sin za ta hada yankunanta, kuma tabbas za su dunkule. Wannan shi ne yanayin tarihi da ba za a iya juyawa ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp