- A Karon Farko Kasashen Sun Yi Magana Da Murya Daya
- Sun Kafa Kwamitin Maka Isra’ila A Kotu
Ganin yadda rikicin Gaza yake ta ci kamar wutar daji, gamayyar Kungiyar Kasashen Musulmi (OIC) da Kungiyar Larabawa (League of Arab States) ta zartar da shawarar dora wa wasu kasashe nauyin shiga tsakani a madadinsu don tabbatar da samun zaman lafiya mai dorewa a yankin Falasdin.
Kasashen za su bi hanyoyin siyasa wajen tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fadin duniya don ganin an kawo karshen cin zali da kashe-kashen da kasar Isra’ila ke yi wa al’ummar Falasdin a Gaza bisa daftarin da Majalisar Dinkin Duniya ta tsara game da yankin, wanda ya bayar da shawarar kafa kasar Falasdin mai cin gashin kanta da kuma ta Isra’ila.
- Gwamnatin Kano Ta Yi Kira A Kwantar Da Hankali Gabanin Hukuncin Kotun Daukaka Kara
- Akwai Kyakkyawan Fata Game Da Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka A Wannan Karo
Daular Saudi Arebiya a matsayinta ta shugabar kungiyar tare da kasashen Nijeriya, Jordan, Masar, Katar, Turkiya, Indonesia, da Falesdin, da kuma duk wata kasa da take da ra’ayin bayar da gudumawar ganin an kawo karshen rikicin Falasdin da Isra’ila sun kudiri aniyar tabbatar da nasarar wannan yunkuri kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tanada.
Wannan na daya daga kudurorin da aka cimma a taron da ya gudana ranar Lahadi 12 ga Nuwamba, 2023.
Haka kuma taron ya nemi mambobin kungiyyoyin su dauki matakan diflomasiya, siyasa da na shari’a don ganin an kawo karshen ayyukan cin zali da kasar Isra’ila ke yi a kan al’ummar Falasdin a Gaza.
Sanarwar bayan taron ta kuma jaddada cewa, “A madadin mu shugabannin kungiyar musulmi ta OIC da kungiyar Larabawa ta ‘League of Arab States’, mun yanke shawarar kiran taron hadin gwiwa na kungiyoyin biyu kamar yadda kasar Saudiya ta nema a matsayinta ta shugabar kungiyoyin biyu. Muna jaddada matsayinmu na yin Allah wadai da hare-haren da Isra’ila take kai wa al’ummr Falasdin a yankin Gaza da masallacin Kudus mai tsarki, muna yin tir da barnar wadannan hare-haren da suka haifar da asarar rayuka da dukiyoyin al’umma mai dimbin yawa.
Mun nemi Isra’ila ta kawo karshen mamayar da ta yi wa kasar Falasdin da kuma kawo karshen dakile musu hakkinsu na walwala, musamman hakkinsu na mallakar kasarsu da iyakoki kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta amince.
“Muna mika godiyarmu ga masu kula da masallatai masu tsarki guda biyu, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, Sarkin Daular Saudi Arebiya, da mai martaba Yarima Mohammed bin Salman bin Abdulaziz Al Saud, Yarima mai jiran gado da kuma Firay Minista a bisa karimcin da suka yi mana.”
Sanawar bayan taron ta kuma ci gaba da bayyana cewa, “Muna tunatar da al’umma a kan dukkan dokokin Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin duniya a kan matsalar Falasdinawa, laifukan yaki da Isra’ila ke aikatawa da kuma bukatar samar wa da Falasdinawa ‘yancin mallakar kasar su da aka mamaye tun a shekarar 1967.
“Muna kuma maraba da shawarar zauren Majalisar Dinkin Duniya mai lamba A/ES-10/L.25 da aka zartar ranar 26 ga Oktoba, 2023.
“Muna jaddada goyon baya ga dukkan masu fafutukar ganin al’ummar Falasdin sun samu ‘yancinsu daga mamayar Isra’ila da kuma hakkinsu na mallakar ‘yantacciyar kasa a karkashin iyakokin da aka tsara a ranar 4 ga watan Yuni na shekarar 1967 da garin Kudus a matsayin babban birinin kasar.
“Muna kuma kara jaddada cewa, in har ana son dawwamammen zaman lafiya wanda kuma shi ne kadai zabi, dole a kawo karshen mamayar Isra’ila tare da aiwatar da shawarar kafa kasashe biyu don kowa ya ci gashin kansa.
“Bai zai yiwu a samar da zaman lafiya a yankin ba ta hanyar kawar da kai daga halin da Falasdin ke ciki, a kan haka muke goyon bayan matakan zaman lafiyar da kungiyar Musulmi ta OIC da kuma ‘Arab League’ ta dauka a kan nema wa Faladin ‘yanci”.
Kasashen sun kuma ce, za su dora wa Isra’ila alhakin ci gaba da hare-haren da ake kaiwa da kazancewar rikicin wanda hakan ya faru ne sakamakon danne hakkin al’ummar Falasdinawa da kuma wurare masu tsarki ga Musulmi da Kiristocin duniya. Wannan kuma ya hada matakai na gallazawa da ci gaba da mamayar kasar Falasdin da kuma karya dokar kasa-kasa wadanda su ne suke dakile duk wani kokarin samar da zaman lafiya a yankin.
“Muna jaddada cewa, Isra’ila ba za ta samu zaman lafiya da cikakkiyar tsaro ba har sai al’ummar Falasdin sun samu nasu tare da kwato musu hakkinsu da aka sace. Tabbas ci gaba da mamayar da Isra’ila ke yi wa Falasdin barazana ce ga tsaro da zaman lafiya yankin da ma duniya baki daya.
“Muna kuma yin tir da duk wani nau’in gaba da wariya da ayuyukan gaba da tsageranci, tare da gargadi a kan sakamakon hare-haren da isra’ila ke kai wa Zirin Gaza wanda tamkar laifukan yaki ne da ake aikatawa ga yankin gabar yamma da kogin Jordan da masallacin Kudus.
“Muna kara gargadi a kan yiwuwar bazuwar yakin in har Isra’ila ta ki dakatar da kai hare-hare a yankin Gaza ko kuma Majalisar Dinkin Duniya ta kasa aiwatar da dokokin kasa da kasa wajen dakatar da hare-haren”.
Haka kuma takardar bayan taron ta yanke shawarar bin hanyoyin siyasa wajen ganin an hukunta Isra’ila a kan dukkan laifukkan yaki da ta aikata a kan Falasdinawa, ciki har da neman shawarar kotun duniya ta hukunta laifukan yaki (ICJ) da kuma matsa lamba wajen ganin kwamitin bincike da Hukumar Kare Hakkin Biladam ta kafa don tattara laifukkan yaki da aka aikata ya yi aikinsa ba tare da takurawa ba.
Haka kuma taron ya yanke shawarar, “Kafa kwamitin ‘yan jarida da za su tattara dukkan laifukkan yaki da Isra’ila ta yi a kan al’ummar Falasdin a hare-haren da take kaiwa tare da fallasawa su a kafafen sadarwa na zamani.
“Muna goyon bayan matakan da kasar Masar ta dauka na fsukantar kasar isra’ila a kan hare-haren da take kaiwa yankin Gaza, muna goyon bayan kokarinta na kai kayan agaji cikin yankin Gaza don tallafa wa al’ummar Falasdin.
Muna kuma kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta dauki tsatsaurar mataki na kawo karshen ayyukan cin zali na Isra’ila da kuma yadda take karan-tsaye ga dokokin Majalisar Dinkin Duniya da kudurin da zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi a ranar 26 ga Oktoba, 2023 mai lamba A/ES-10/L.25, za mu dauki rashin katabus na aiki da kudirin a matsayin hadin baki na ba da damar ci gaba da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ciki har da yara, mata da tsofafi, da kuma mayar da Gaza tamkar kufai”.
Kungiyar ta kuma nemi kasashen duniya su dakatar da kai wa Isra’ila makaman da take amfani da su wajen lalata gidaje, asibitoci, makarantu, masallatai da coci-coci da kuma duk wani abin amfani a yankin Falasdinawa.
Sun kuma nemi majalisar Dinkin Duniya ta gaggauta zartar da kudurin yin tir da Isra’ila a kan hare-haren da ta kai asibitoci a yankin gaza da kuma katse shigo da magunguna, abinci, man fetur da wutar lantarki, ruwa da kafafen sadarwar na Intanet.
“Wannan laifukan yaki ne a karkashin dokokin kasa da kasa, muna kira da a tabbatar da hukunta Isra’ila a bisa wadanna laifukan. Muna kuma mika bukatar a dage kawanyar da Isra’ila ta yi wa Gaza na tsawon shekaru.”
Hakazalika, takardar bayan taron ta nemi mai gabatar da kara na kotun ICC ya hanzarta kammala bincikensa na laifukkan yaki da Isra’ila ta aikata a kan Faladinawa, da yin kira ga sakataren OIC da na Arab League su bibiyi yadda lamarin ke gudana tare da tattara miyagun laifukan da Islra’ila ta aikata a Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023.
“Muna yin tir da tarwatsa Falasdinawa fiye da rabin miliyan daga arewaci da kudancin Gaza a matsayin laifukkan yaki kamar yadda doka ta hudu na taron Geneba na shekarar 1949 da 1977 ta tanada, muna kira ga duk kasar da ta sanya hannu a kan dokar ta yi tir da Isra’ila a kan karya dokokin da ta yi, da kuma gaggauata bude kofar mayar da al’umma gidajensu, tare da sakin dukkan fursunonin yaki”.
Kungiyoyin kasashen, sun kuma yi Allah wadai da kashe ‘yan jarida, yara da mata da ma’aikatan lafiya da kuma amfani da makamai masu guba da aka haramta amfani da su kamar ‘white phosphorus’, wanda Isra’ila ta yi amfani da su a yanki Gaza da Labanan, da kuma tir da miyagun kalamai na barazana da jami’an Isra’ila ke yi.
“Muna karfafa kudurinmu na samar da zaman lafiya a tsakanin Larabawa da Isra’ila kamar yadda dokokin kasa da kasa suka shimfida, ciki har da kudurorin Majalisar Dinkin Muniya masu lamba 242 (1967), 338 (1973), 497 (1981), 1515 (2003), and 2334 (2016); wadanda suka nemi a kawo karshen dukkan mamayar da aka yi wa Falasdin da kuma zamanta cikakkiyar kasa kamar yadda aka zartar a ranar 4 ga Yunin 1967,ya kuma hada da bayar da diyya ga Falasdinawa ‘yan gudun hijira kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta zartar a kudurinta na 194 da aka zartar a shekarar 1948.”
Daga bisani kungiyoyin sun nemi a gaggauta kiran babban taron kasa da kasa don karfafa aiki da dokokin Majalisar Dinkin Duniya da kudurorin da ta zartar a shekarun baya don kawo karshen mamayar da Isra’ila ta yi wa yanki Falasdin tun a shekarar 1967, haka kuma a tabbatar da samar da kasashe biyu wanda kowa ke cin gashin kansa.
Daga nan kuma sun nemi kasashen duniya su zabura don tattara tallafi tare da kaiwa yankuna Falasdinawa ta hannun gwamnatin Faladin da kuma kungiyar majalisar dinkin duniya mai kula da bayar da agaji.
Kasashen sun kuma ce za a nemi gudummawar al’ummar duniya don sake gina sassan Gaza da Isra’ila ta ragargaza.