Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya gabatar da jawabi ta bidiyo, domin mika gaisuwa ga duniya yayin da ake gab da shiga sabuwar shekarar gargajiya ta al’ummar Sinawa, wato Shekarar Maciji.
Antonio Guterres ya nanata cewa, maciji na alamta hikima da juriya da farfadowa. Ya kuma karfafawa al’ummar duniya gwiwar rungumar sabuwar shekarar da kyakkyawan fata da jajircewa da nufin samar da kyakkyawar makoma ga kowa da kowa. Ya kara da fatan samun koshin lafiya da farin ciki da wadata da sabon mafari a Shekarar ta Maciji. Har ila yau, ya godewa kasar Sin da al’ummarta, bisa goyon baya mai karfi da suke ba MDD da tsarin hadin gwiwar kasa da kasa da ma hadin gwiwar duniya baki daya. (Fa’iza Mustapha)