Daga tafiyar Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zuwa kwanakin farko na wa’adin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu an samu sake barkewar matsalar tsaro abin da har zuwa rubuta wannan sharhin babu abin da ya canza sai dai ma karuwar da aka samu.
Tun daga yankin Arewa ta tsakiya, Arewa maso Gabas, Arewa maso yamma, Kudu maso Kudu da yankin Kudu maso Gabas, dukkan bangarorin siyasar nan 6 na fuskantar nasu nau’in matsalar da ke bayyana a mastayin ‘yan ta’adda, masu garkuwa da kuma ‘yan bindigan da ba a sani ba.
- Chelsea Ta Dauki Mai Tsaron Raga Daga Brighton
- Shugabancin APC: NEC Za Ta Bayyana Matsayar Ganduje A Yau
Rahottanni daga yankin Arewa maso Gabas yana nuna yadda kauyukan Jihar Borno musamman manoma, a halin yanzu suna nan a karkashin mulkin ‘yan kungiyar Boko Haram kungiyar ‘yan ta’addan nan da ta addabi al’umma. Rahottanin kafafen yada labarai na nuna yadda aka samu karin kashe-kashe a yankin gaba daya. Jihohin Benuwai da Filato da ke yankin Arewa ta tsakiya sun zama mahauta da ake kashe mutane a kullum, ‘yanta’adda dauke bindiga suke cin karensu babu babbaka da suna makiyaya, suna kai hare-hare a cikin dare sunan kashe mutane babu kakkautawa. A wani jawabin da ya yi kwanan nan, Gwamnan jIhar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi korafin cewa, a halin yanzu ‘yan ta’adda daga Jihar Filato suna neman mamaye jiharsa. Shi ne shugaban tsaro a jihar, a kan haka al’umma na tsananin bukatar ya dauki matakin da ya kamata don kawo karshen matsalar tsaron da al’umma jihar ke fuskanta.
Ana cikin wannan halin ne kuma sai gashi jami’an tsaro sun kama mota shake da bindigogi da albarushi ta taso daga yankin kudu maso gabas an kama ta a cikin Jihar Ogun. Kwanakin baya ne kuma mataimnakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya sanar da cewa, a halin yanzu gwamnati ta samar da hanyoyi da dama masu inganci da za su yi amfani da su wajen magance matsalolin tsaro da ake fuskanta a sassan kasar nan. Haka kuma a taron da ya yi da shugabanin rundunonin tsaro, shugaban kasa, Tinubu ya umarce su da su dauki tsattsaurar mataki wajen tabbatar da tsaro a sassan Nijeriya ba tare da bata lokaci ba.
A wani ra’ayinmu da muka gabatar kwanakin baya, mun bukakaci jami’an tsaro da takura ‘yan ta’adda tare da samar da zaman lafiya a duk inda suke. Wannan yana zuwa ne a matsayin martani ne ga umarnin da shugaban rundunar sojojin Nijeriya, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya ba dakarunsa na su matsawa ‘yan ta’adda don a cewarsa lokacin tattaunnawa ya wuce amma kuma har zuwa wannan lokacin lamarin bai sake zani ba don kuwa ‘yan ta’addan na nan na ci gaba da gallaza wa al’umma a ssassan Nijeriya ba tare da tausayawa ba.
A matsayinmu na gidan jarida hankalinmu a tashe yake a kan yadda ake kashe-kashe a kasar mu. Hankalinmu a tashe yake musamman saboda ganin yadda har zuwa yanzu ba a yi abin da ya kamata a yi ba, in ban da surutai da bayar da umarnin da ake kasa cikawa. Don haka muna kira ga sabbin shugabanni rundunonin tsaro da su maida wajen cika alkawauran da suka yi na kare al’umma da dukiyoyinsu.
Hankalinmu na kara tashi ne saboda ganin yadda ‘yansiyasa ke nuna halin ki inkula a kan matsalar tsaron da kasa ke fuskanta, hankali na kara tashi ne kuma in aka lura da yadda suka mayar da hankali a kan jin dadinsu ta hanyar saya wa kansu manyan motoci masu sulke a kan kudade masu yawan gaske, wannan ya kai ga zargin cewa, ‘yan ta’addan na gallaza wa al’ummar Nijeriya ne bayan da ‘yan siyasa suka yi watsi da su bayan sun yi amfani da su a matsayin ‘yan banga a gangamin siyasan da aka yi kwanakin baya.
Ire-iren wanan ne ke kara tabbatar wa masu sharhi a kan al’amurran yau da kullum ne a halin yanzu harkar tsaro ta zama wata kasuwancin biliyoyin naira, shi yasa kowa ke neman ya samu rabonsa, musamman ganin ana ware makudan kudi a kasafin kudin shekara-shekara wanda kuma har yanzu an kasa inda kudaden ke shiga a duk shekara.
In har ba haka ba ne, to ‘yan ta’addan na amfani da yadda harkokin jami’an tsaron kasar ya sukurkure suke cin karensu babu babbaka. Abin lura a nan shi ne kamar ana yi wa jamai’a ritaye ne a mika ragamar tafiyar runduna ga sabbi su kuma kuma su bata lokaci mai tsawo wajen sanin makomar aiki, a na kuma zargin su da karkatar da dimbin kudaden da aka ware wajen azurta kansu. A kan haka ya kamata su fahimci cewa, al’ummar Nijeriya sun zura ido na ganin aiki ba wai surutu ba.
A ra’ayinmu, ko ma menene matsalar tsaron da ake fuskanta a Nijeriya, ‘yan Nijeriya suna jiran ganin ana aiki ne da zai tabbatar da tsaron rayuwa da dukkiyoyinsu. In har akwai gwamnati a matakin tarayya, jihohi da kananan hukumomin, to daya daga cikin manyan aikin da tsarin mulki ya dora masu shi ne kare rayuwa da dukiyoyin al’umma. Ba mu yarda da duk wani kauce-kauce ba aiwatar da aikin da tsarin mulki ya dora masu.