Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake kare shirin sauya fasalin Naira da babban bankin Nijeriya CBN ya yi gabanin zabukan 2023 da kakkausar murya inda ya bayyana cewa, shirin ya haifar da gudanar da sahihin zabe.
Buhari ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da wani littafi mai taken “Aiki tare da Buhari: rawar da hadimi na musamman ya taka kan harkokin yada labarai (2015 – 2023)” da aka yi a Abuja.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, wani tsohon mai taimaka wa Buhari, Femi Adesina ne ya rubuta littafin
Buhari ya yi dogon bayani game da sake fasalin kudin Naira mai cike da cece-kuce, ya kuma bayyana dalilin da ya sa bai kori tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ba a lokacin da fastocinsa na neman shugabancin kasar suka bayyana a fadin kasar.
Ya kara da cewa, in ya kori Emefiele bai masa adalci ba tun da tsohon Gwamnan CBN bai sanar da shi ko wasu mukarrabansa ba game da aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa a 2023.
Ya kuma musanta zargin da ake yi masa na haddasa karancin Naira domin hukunta ‘yan Nijeriya, inda ya ce, bai yi hakan don muzguna wa kowa ba.