Akalla mutane bakwai ne ake fargabar mutuwarsu sakamakon harin da wasu mahara suka kai wa al’ummar Kudu a Karamar Hukumar hukumar Toto ta Jihar Nasarawa.
Kudu, al’ummar Gbagyi ke zaune a yankin, an kai musu harin ne a ranar Lahadin da ta gabata, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka da dama.
- Almundahana: An Gano Karin Biliyan 3 Da Ta Sake Batan Dabo Karkashin Betta Edu
- Soyayyar Kananan Yara: A Ina Gizo Yake Sakar?
Wata majiya ta bayyana cewa gidaje da dama sun kone, sannan mutane da dama sun tsere daga gidajensu sakamakon harin.
Wata majiyar ta danganta lamarin da rikcikin da ke tsakanin kungiyar Bassa da al’ummar Gbayi.
Rikicin da aka dade ana fama da shi tsakanin kabilun Igbirra da Bassa a yankin Karamar Hukumar, ya shafe tsawon shekaru ana kai ruwa rana.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana shirin magance matsalar tsaro, tare sa shiga tsakani kan lamarin.
Yayin da aka tura hukumomin tsaro zuwa yankin, gwamnan ya shirya kiran taro tsakanin al’ummomin Gbagyi, Egbirra, da Bassa don magance rikicin da ke tsakaninsu.
“Hukumomin tsaro sun riga sun shiga tsakani. Dole ne mu kawo karshen wannan rikici,”in ji shi.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar , DSP Ramhan Nansel, bai samu damar amsa kiran wakilinmu kan lamarin ba.