A shekarun baya bayan nan, ana ta ganin karuwar sabani, da rashin daidaito ta fuskar alakar Sin da Amurka, wanda hakan ke da matukar hadari ga dunkulewar duniya da cimma nasara tare.
A halin yanzu, yanayin alakar kasashen biyu na cike da kalubale, ya kuma gaza hawa turba mai inganci da za ta haifar da moriya ga sassa biyu da ma duniya baki daya. Hakan ya sa masharhanta ke ganin lokaci ya yi manyan kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, za su rungumi hanyoyin da ba na fito na fito ba, wajen shawo kan mummunar takara, su kuma amince da tafarki guda na cimma nasara wadda kowa zai ci gajiyarta.
- Xi Ya Taya Trump Murnar Lashe Zaben Shugaban Amurka
- Sin Ta Yi Alkawarin Fadada Bude Kofa Da Hadin Gwiwa Da Kasa Da Kasa
A ganina, hanya daya tilo ta kaiwa ga cimma wannan nasara ita ce dukkanin sassan biyu su amine cewa za su iya bin hanyoyin cimma daidaito cikin lumana, da tattaunawa, wadanda za su dace da zaman jituwa da moriyarsu.
Yayin da Sin da Amurka ke kara fadada tasirinsu ta hanyar karfafa alaka da sauran sassan duniya, fifikon Amurka shi ne karfin ikon ayyukan soji, da samar da kariyar tsaro ga kawayenta da tasiri a siyasar duniya. A hannu guda kuwa, kasar Sin na mayar da hankali ne ga fadada zaman jituwa, da zuba jari, da ingiza cinikayya tsakaninta da sauran kasuwannin duniya.
Kafin shekarar 2001, wato shekarar da kasar Sin ta shiga kungiyar cinikayya ta duniya ko WTO, kaso 80 bisa dari na kasashen duniya suna gudanar da hada-hadar cinikayya ne da Amurka sama da yadda suke yi da kasar Sin. Amma a yau, manufofin kasar Sin irin su shawarar nan ta “Ziri daya da hanya daya, sun haifar da fadadar cinikayya tsakanin Sin da kasashen duniya 128 cikin 190 sama da yadda suke yi da Amurka.
Nan gaba kadan za a kafa sabuwar gwamnatin Amurka, kuma fatan al’ummun duniya shi ne wannan sabuwar gwamnati ta zo da tsarin sassanta alaka da Sin, ta yadda hadin gwiwarsu za ta ingiza daidaito, da ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya. Kana duniya ta ci gajiya daga nasarar da kyautatuwar alakar manyan kasashen biyu za ta haifar. (Saminu Alhassan)