Ɗan wasan bayan Arsenal, William Saliba, ya amince da sabon kwantiragin shekaru biyar da zai ci gaba da zama a ƙungiyar har zuwa shekarar 2030.
A halin yanzu, kwantiraginsa na yanzu zai ƙare ne a 2027.
- An Yi Bikin Nune-Nunen Hotuna Da Bidiyo Na MDD Da Bikin Kade-Kaden Fina-Finai Masu Alaka Da Zaman Lafiya A Birnin New York
- Gwamnatin Katsina Ta Bankaɗo Ma’aikatan Bogi 3,488
Saliba, mai shekara 24, ya koma Arsenal daga Saint-Etienne a 2019.
Daga baya aka kai shi aro a Nice da Marseille kafin ya dawo ya zama ginshiƙin tsaron ƙungiyar a ƙarƙashin mai horaswa Mikel Arteta tun 2022.
Ya buga wa Arsenal wasanni 137 zuwa yanzu.
Sabon kwantiragin ya nuna Arsenal na son kare shi daga ƙungiyoyi manya na ƙasashen Turai irin su Real Madrid da Manchester United.
Arteta na fatan hakan zai taimaka wajen cika burinsa na lashe gasar Firimiya.
Haka kuma, abokin Saliba a tsaron baya, Gabriel Magalhães, ya tsawaita kwantiraginsa har zuwa shekarar 2029.
Arsenal za ta kara da Newcastle a filin St James’ Park a ranar Lahadi, inda ake sa ran haɗin Saliba da Gabriel zai ƙara ƙarfafa bayan ƙungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp