Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da yi wa Nijeriya addu’a.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Mista Edwin Olofin, ya fitar a ranar Talata a Abuja, Ganduje ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da su yi addu’a ga shugaban kasa Bola Tinubu domin cika alkawarin da ya daukar wa ‘yan Nijeriya.
- Sallah Ƙarama: Abun Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sallar Idi Da Ladubanta
- Sallah: Gwamnatin Katsina Ta Yi Wa Fursunoni 222 Afuwa
Bayanin na zuwa ne domin taya al’ummar Musulmi murnar sallah, wanda ke nuna karshen azumin watan Ramadan.
Shugaban jam’iyyar APC, ya bukaci al’ummar Musulmi da su rika yin koyi da darusan da suka koya a watan Ramadan a domin kyautata mu’amalar yau da kullum.
“Hakika watan Ramadan wata ne na hakuri. A cikinsa muna yin azumi don Allah ta hanyar jure yunwa da kishirwa, kuma muna tallafa wa marasa galihu,” in ji shi.
Ya gode wa Musulmai bisa addu’o’in da suke yi wa kasa da kuma Shugaba Tinubu, ya kuma bukace su da su ci gaba da yin addu’o’i ba dare ba rana.
“Ina kira ga daukacin ‘yan Nijeriya, ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba, da su mara wa shugabanmu baya.
“Duk masu hankali sun san cewa Shugaba Tinubu ya dauki tsauraran matakai don gyara tattalin arzikinmu.
“Abin da muke bukata a yanzu shi ne mu tallafa wa Gwamnatin Tarayya don kawo sauyi a kasar nan,” in ji shi.