An ce idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi, tun da shekarar 2024 ta fara yin adabo, kasashe na ta yi wa kansu hisabi a kan abubuwan da suka shuka a cikin shekarar. Na tabbatar da cewa, wadanda suka shuka alheri ko gizau, daidai da kwayar gashin girarsu daya ba ta karaya ba. Haka nan ’yan baya-ga-dangi masu tafka ta’asa su ma sun san kansu, domin kowa ya gyara ya sani, kazalika kowa ya bata ya sani.
A yayin da wasu kasashe musamman masu karfin fada-a-ji a duniya suke taimakawa da makamai wajen yi wa al’ummar da ba ta ji ba, ba ta gani ba kisan kiyashi, ita kuwa kasar Sin ta nuna himma wajen shimfida fukafukanta ga sassan duniya wajen samar da ci gaba da raya duniya da tsare-tsare mafiya dacewa da zamanin da muke ciki.
- Wannan Jawabi Ya Karfafa Zuciyarmu a Fannoni Uku
- Tashar Samar Da Wutar Lantarki Mai Amfani Da Karfin Ruwa Mafi Girma a Duniya Ta Fara Aiki
A shekarar 2024, kasar Sin ta karbi bakuncin manyan tarurruka na hadin gwiwa da shugabannin kasashen duniya kamar su taron dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa a watan Mayu, da babban taron cika shekaru 70 da kafa ka’idojin dorewar zaman lafiya a watan Yuni da kuma taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka a watan Satumba.
Kazalika, daga waje, Shugaba Xi Jinping na kasar ya kai ziyarce-ziyarce masu muhimmanci kasashen ketare da suka hada da yankin Turai a watan Mayu, yankin tsakiyar Asiya a watan Yuli da yankin Latin na Amurka a Nuwamba, baya ga taron kawancen kasashen BRICKS da ya halarta a watan Oktoba.
Duka a tarurrukan da kasar Sin ta karbi bakuncinsu a cikin gida ko shugabanninta suka halarta a ketare, an mayar da hankali a kan kyautata hulda da hadin gwiwar samar da ci gaba mai gamewa da kuma wanzuwar adalci a tsakanin kasashe da shugabancin duniya.
A karon farko a yankin Turai, kasar Serbia ta amince da shiga kokarin gina al’umma mai makoma ta bai-daya a sabon zamani. Bugu da kari, Sin ta bude sabon babi na huldarta da Faransa yayin da Shugaba Xi ya ziyarci kasar a watan Mayu. Haka nan, ta daga darajar alakarta da Hungary, baya ga ci gaba da tuntubar juna da tattaunawa da sauran kasashen yankin kamar su Jamus, Birtaniya, Spain, Italiya da hatta Amurka ma Sin ta nemi kara kyautata huldodinsu cikin lumana yayin da Shugaba Xi da Shugaba Biden suka yi ganawar keke-da-keke a birnin Lima na Peru a watan Nuwamba, a gefen taron APEC.
Kazalika, Sin da Afirka sun dora tubali na gina al’umma mai makoma ta bai-daya a dukkan sassa da zai game mutanensu biliyan 2.8.
A yankin makwabta ma, alakar Sin da kasashe ta kara karfi inda aka fara wata sabuwar kyakkyawar hulda tsakanin Sin da Vietnam a shekarar ta 2024. Haka nan, fitar farko zuwa waje da zababben shugaban kasar Indonesia Prabowo Subianto ya yi, ita ce zuwa kasar Sin a watan Oktoba. Kana, Sin da Malaysia sun yi bikin cikar huldarsu ta diflomasiyya shekaru 50 da kafuwa, sannan alakar kasar da sauran kasashe irin su Singapore, Laos da Cambodia duka sun inganta cikin zurfafawa. Yayin da har ila yau, manyan kasashen yankin irin su Japan da Indiya duka suka amince su rika tuntubar juna da wanzar da zaman lafiya a kan iyakokinsu. Sakamakon haka ne Sin da Japan suka amince su gaggauta aiwatar da shawarar da aka cimma dangane da fitar da dagwalon masana’antu na Fukushima ba tare da bata lokaci ba, yayin da Shugaba Xi ya gana da firaministan Japan Shigeru Ishiba, a gefen taron shugabannin mambobin APEC karo na 31.
Kasar Sin ta kasance a gaba wajen yekuwar hawa teburin sulhu da tattaunawa maimakon fito-na-fito kan duk wata mas’ala da ta taso a duniya har ma ya kai ga babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 ya amince da kudurin da Sin ta gabatar na kebe ko wace ranar 10 ga Yuni ta zama ranar tattaunawa a tsakanin wayewar kai da al’adu na mabambantan kasashe.
Haka nan, ta rika kai goro-ta-kai-mari wajen tabbatar da amincewar kudurin tsagaita bude wuta a yankin Gaza na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da sulhunta bangarorin Falasdinawa da kaddamar da kungiyar “abokan neman zaman lafiya” dangane da rikicin Ukraine.
Domin dorewar ci gaban duniya da kawo sauyi mai ma’ana, Shugaba Xi ya nanata matsayin Sin na bin turbar zaman lafiya a ko yaushe, yayin da yake maraba da jakadun kasashe 28 da suka fara aiki a kasar Sin a watan Disambar 2024. Inda hakan ya nuna bambanci a fili tsakanin Sin da manyan kasashe masu tayar da husuma a kan iyakokin teku, da bayar da makamai na kisan kare dangi a yankunan da ake rikici da zama kanwa-uwar-gamin galibin fitintinun da ake fama da su a duniya.