Ga duk mai bibiyar ci gaban da kasar Sin ta samu musamman a gwamman shekarun da suka gabata, tilas ya amince cewa salon da kasar ke bi wajen zamanantar da kai ya ciri tuta, duba da yadda ya haifarwa ’yan kasar da mai ido ta fuskar tsame alumma daga kangin talauci, da samarwa alummar Sinawa damar more ababen more rayuwa masu inganci, da raya fasahohin zamani da sauransu, wadanda dukkanin su ke zama muhimmin misali mai kima ga sauran kasashe masu tasowa musamman na Afirka.
Kasashen Afirka na iya koyi da dabarun kasar Sin ta fuskar aiwatar da managartan manufofin raya kai, da gudanar da sauye-sauye da zamanantarwa, ta yadda su ma za su daga matsayin su daga kasashen da alummun suke fama da karancin karfin tattalin arziki zuwa cibiyoyin raya tattalin arziki a matakin kasa da kasa.
- Xi Ya Mika Gaisuwar Ban Girma Ga Dattawa A Jajibirin Ranar Tsofaffin Kasar Sin
- Ban Yi Nadamar Yakar PDP A Zaben 2023 Ba – Wike
Mun dai ga misalan hakan a bangaren kasar Sin, wadda ta kawar da fatara, da cike gibi tsakanin mawadata da masu rauni, zuwa wanzar da ci gaba mai dorewa a dukkanin fannoni, matakan da suka kai kasar zuwa turbar samun ci gaba a dukkanin bangarori, da daidaita tafiya tsakanin raya tattalin arzikin kasa da ci gaban zamantakewa da walwalar alumma.
A daya hannun, muna iya cewa yadda kasashen Afirka ke kara rungumar tafiyar samar da ci gaba tare da kasar Sin, karkashin tsare-tsare, da dandaloli daban daban abun a yaba ne. A duk inda muka duba muna iya ganin ayyukan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka na raba ababen more rayuwa, da musayar kwarewa, da musayar aladu, da karfafa kawance, da bunkasa cinikayyar hajoji da hidimomi tsakanin sassan biyu.
Baya ga hakan, wasu karin sassa da ya kamata sassan biyu su inganta hadin gwiwa su ne batun samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da kare muhallin halittu, da rage tasirin dumamar yanayi, da raya samar da makamashi mai tsafta, fannonin da tuni kasar Sin ta yi nisa a fannin cimma nasarar su.
Yayin da ake duba yiwuwar fadada kawance, da cudanya tsakanin Sin da kasashen Afirka a dukkanin fannoni, wajibi ne a jinjinawa yadda Sin din ke fadada tallafin da take baiwa kasashen Afirka ta fuskoki da dama, kamar samar da yankunan raya masanaantu, da yankunan cinikayya maras shinge, da taimakon raya fasahohin noma na zamani da dai sauran su.
Kaza lika, ya zama dole a yabawa kasar Sin don gane da sabbin shirye-shiryen hadin gwiwa 10 da ta gabatar a baya bayan nan, don ingiza zamanantar da kasashen Afirka abokan tafiyarta, shirye-shiryen da ko shakka babu za su yaukaka dunkulewar ayyukan hadin kan sassan biyu, kana sun dace da ajandar raya nahiyar Afirka ta nan zuwa shekarar 2063, da ma ajandar raya yankin cinikayya maras shinge na daukacin kasahen Afirka.