Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabiru Yusuf, ya ce; ba shi da masaniya kan abin da ya faru a Unguwar Rimin Zakara da ke Karamar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane uku da jikkata mutane da dama a yankin a sakamakon rusau da aka gudanar a yankin.
Gwamnan ya ce, “Sai shekaran-jiya cikin dare na samu labarin abin da ya faru. Ashe tsohuwar rigima ce ta kusan shekaru 30, tsakanin Jama’ar Rimin Zakara da Jami’ar Bayero”
- Sin Na Maraba Da Baki Daga Daukacin Duniya Su Zo Su More Da Kyawawan Al’adun Sinawa
- Gidaje Da Dabbobi Sun Ƙone A Yayin Da Gobara Ta Tashi A Wani Ƙauyen Kano
Gwamna Abba ya ce; nan take ya dauki matakin dakile fitinar tare da daukar matakan dakatar da ita cikin gaggawa.
Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025.
A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan yankin da Jami’ar Bayero. Gwamnan ya yi kuma alkawarin samar da Asibitin sha-ka-tafi da samar musu da hanya da kai hasken wutar lantarki da rijiyoyin burtsatsai da bai wa iyalan mamatan jari da daukar dawainiyar karatun yaransu gwargwadon iko da kuma daukar nauyin jinyar wadanda suka ji rauni a yankin a yayin rusau da aka yi a makon da ya gabata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp