Dattijo, Uban kasa kuma fitaccen dan kasuwa, Aminu Alhassan Dantata, ya bayyana cewa sam yanzun ya daina jin dadin rayuwa, burinsa kawai fatan ya hadu da Allah cikin aminci da Imani.
Dantata, mai shekaru 91, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima.
Ya ce tun yana matashi, Allah ya bashi damar haduwa da mutane da dama kuma ya kulla abota da su amma da kyar zai iya kiran mutum 10 da su ke raye a yanzun.
“Na zagaya duk jihohin Nijeriya kuma na yi abubuwa da mutane a duk jihohin, da yawansu abokaina ne amma abin bakin ciki, duk mutanen da na sani, da kyar na iya kiran mutum 10 da ke raye.
“Gaskiya, kamar yadda nake a yanzu, ina jira kawai lokacina ne ya yi. Bana jin dadin rayuwa. Ina fatan barin duniya da imani.” Inji Dantata.