Sama da kamfanoni 5,600 daga ciki da wajen kasar Sin ne suka hadu a Shanghai domin halartar baje kolin sassan motoci da kayayyakin aiki da hidimomi na kasa da kasa.
An fara baje kolin wanda shi ne karo na 18, a ranar Laraba, inda zai gudana har zuwa gobe Asabar 2 ga watan Disamba.
- Sin Da Japan Da Koriya Ta Kudu Sun Sake Karfafa Huldar Diflomasiyya
- An Bukaci Koriya Ta Kudu Ta Nemi Gafarar Musayar Wutar Tekun Koriya Ta Arewa
Masu baje hajoji sun fito ne daga kasashe da yankuna 41, ciki har da Amurka da Poland da Jamus da Faransa da Spaniya da Italiya da ma Birtaniya.
Alkaluma daga kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin sun nuna cewa, adadin motocin da aka samar a kasar tare da sayarwa, ya kai miliyan 24 a dukkan bangarorin biyu. Kuma idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, an samu karuwar kaso 8 a bangaren samarwa da kaso 9.1 a bangaren sayarwa. ( Fa’iza Mustapha)