Sama da kasashe da hukumomin kasa da kasa 70 ne suka ba da tabbacin za su halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin na kasa da kasa, karo na 7.
A cewar mashirya bikin, ana sa ran adadin masu baje koli zai zarce na bikin karo na 6. Bikin, wanda aka shirya zai gudana daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba, zai karbi bakuncin kasashen Norway da Slovakia da Benin da Burundi da Madagascar da Asusun UNICEF mai kula da kananan yara, a karon farko.
Bugu da kari, rumfar kasar Sin za ta gabatar da manyan nasarorin da aka samu wajen zurfafa gyare-gyare a kasar, tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)