Bayanai daga ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin sun nuna a ranar Lahadi cewa, fiye da masu amfani da kayayyakin laturoni miliyan 20 ne suka nemi shiga tsarin nan na samar da rangwamen gwamnati, ta musayar tsoffin kayayyakin laturoni da sabbi na kasar Sin, tun bayan da gwamnatin kasar ta kaddamar da shirin na samar da kayayyaki makonni uku da suka gabata.
Bayanan sun nuna cewa, a ranar Asabar, an samu kimanin masu amfani da kayayyaki miliyan 20.09 da suka nemi tallafin don sayen kayayyaki guda miliyan 25.41 na kayayyakin laturoni kamar wayoyin hannu.
- Xi Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Shugaban Namibia Na Farko
- Kasafin 2025: Kar A Yi Sakaci Macizai Da Birai Su Haɗiye Dala Biliyan 1.07 Da Aka Ware Wa Kiwon Lafiya – Atiku
Tun daga ranar 20 ga watan Janairu ne, kasar Sin ta fara ba da tallafin karkashin tsarin nan na samar da rangwame, ta musayar tsoffin kayayyakin laturoni da sabbi, a daidai lokacin da kasar ta kara fadada shirin na musayar tsoffin kayayyakin masarufi da sabbi, don kara habaka sayayyar kayayyakin amfanin gida, wanda ke baiwa masu amfani da kayayyaki rangwamen da ya kai yuan 500 kwatankwacin dalar Amurka 69.7 kowane mutum daya kan sayen kayayyakin amfani na zamani.
Katafaren kamfanin nan na biyan kudi da kati na kasar Sin wato UnionPay ya bayyana cewa, a cikin lokacin da aka bayar da rahoton, an yi ciniki mai rangwame na kudi miliyan 6.27 da ainihin darajar ta kai yuan biliyan 20.58.
Sakamakon tallafin gwamnati, adadin cinikin wayar hannu a kasar Sin ya karu da kashi 74 cikin dari, yayin da darajar ciniki ta kai kashi 65 cikin dari a kowane mako, a makon dake kafin bikin bazara, wanda aka yi a ranar 29 ga watan Janairun bana, kamar yadda bayanan kasuwar suka nuna. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp