• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Samar Da Hanyoyin Tabbatar Da Tsaro A Duniya Da Inganta Amincewa Da Juna A Taron Dandalin Tsaro Na Xiangshan 

by CGTN Hausa
2 years ago
Xiangshan

Bisa la’akari da batutuwan tsaro da dama da duniya ke fuskanta, taron dandalin Xiangshan na birnin Beijing na kasar Sin karo na 10 ya kasance daya daga cikin muhimman tarukan tsara manufofin tsaro tare a duk duniya. A bana, mahalarta taron za su yi zama a nan birnin Beijing, domin tattauna batutuwan farko dake fuskantar tsaron kasashen duniya.

 

Yaki da kalubalen tsaro da ke kunno kai daga wurare da lokutan da ba a yi hasashensu ba, na iya taimakawa wajen hada kan masu ruwa da tsaki a kan manufa daya, yayin da suke da ikon yin hadin gwiwa yadda ya kamata kan wadannan matsalolin da suke gurgunta ci gaban kasashen duniya musamman kasashe masu tasowa. Duk da haka, wannan dandalin tsaro zai bankado cikakkun matakan tsaro don inganta zaman lafiya da bunkasuwa, da wadata ga dukkanin kasashe. Da tabbatar da duniyar zaman lafiya da kwanciyar hankali mai amfanar dukkan al’ummomi.

  • Xi Ya Jaddada Bukatar Karfafawa Mata Gwiwa Domin Bayar Da Gudunmowarsu Ga Zamanantar Da Kasar Sin
  • Hun Manet: Kasar Kambodiya Na Goyon Bayan Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”

Tun kafuwar dandalin a shekara ta 2006, dandalin tsaro na Xiangshan na Beijing, wanda ke kiyaye ka’idojin “Daidaito, Bude kofofi, Hadin kai, musayar ra’ayoyi”, ya zama wani muhimmin dandalin tsaro na kasa da kasa. Dandalin yana daga cikin manyan tarukan tattaunawa kan manufofin tsaro na kasa da kasa a duniya, ta hanyar bude kafar tattaunawa don magance batutuwan da suka shafi tsaro na duniya, da habaka hadin gwiwa, da karfafa amincewar juna. Har ila yau, yana baiwa kasashe masu tasowa damar bayyana ra’ayoyinsu da kuma shiga harkokin tafiyar da harkokin tsaron duniya. Kasar Sin ta dauki nauyin dandalin ne domin inganta ra’ayoyinta kan muhimman batutuwan tsaro na kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da shirya tattaunawa da jami’an mahalarta taron.

Taron dandalin na bana, mai taken “Tsaro na bai daya, zaman lafiya mai dorewa” ya mai da hankali kan shawarar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen duniya kan batun tsaro, yana baiwa dukkanin bangarori damar bayyana ra’ayoyinsu bisa daidato da adalci. Har ila yau, ana tattauna matsalolin tsaro, da bin hanyoyin samar da tsaro, da inganta hadin gwiwar tsaro. Za a gudanar da tarukan musamman guda takwas a lokaci guda da kuma zama hudu a dandalin na bana. Haka kuma, za a gudanar da turakan karawa juna sani a fannonin tsaro daban-daban musamman taron karawa juna sani na jami’an tsaro matasa da malamai masana harkokin tsaro.

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

Taron na dandalin tattaunawa na Xiangshan na Beijin karo na 10 dake gudana daga ranar 29 zuwa ranar 31 ga watan Oktoba ya hada tawagogin hukuma daga kasashe sama da 90 da kungiyoyin kasa da kasa, gami da wakilai 22 a matakin ministan tsaro ko sama da haka, da wakilai 14 a matakin hafsan soji. Kana, fiye da masana 200 daga kasashe da yankuna sama da 50 sun nemi shiga dandalin. (Muhammed Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika
Daga Birnin Sin

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Gaza
Daga Birnin Sin

Wane Ci Gaba Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza Ta Haifar?

October 16, 2025
Next Post
Ziri daya

Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Ta Amfanawa Al’ummar Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

October 17, 2025
peter

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

October 17, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

October 17, 2025
Tinubu

Batun Yin Afuwa Ga ‘Yan Yankin Ogoni Huɗu

October 17, 2025
Shettima

‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima 

October 17, 2025
Manzon Allah

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

October 17, 2025
An Kashe Mutane Da Dama Da Kone Gidajensu A Wani Hari Da Aka Kai Benuwai

Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma

October 17, 2025
Shugaban Najeriya Ya Kaddamar Da Aikin Samar Da Ruwa Da Kamfanin Sin Ya Gudanar A Birnin Abuja

Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura

October 17, 2025
Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027

October 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.