A makon da ya gabata ne aka gudanar da bikin ranar yara ta duniya. Rana ce da aka ware don jawo hankalin al’umma a kan halin da yaran Nijeriya ke ciki, musamman ganin dukanmu mun taba kasance wa yara a wani lokaci na rayuwarmu.
Biki ne da ke da matukar muhimmanci don yana tunatar da mu bukatar kula tare da samar da kariya ta musamman ga yara don ta haka ne za mu tabbatar da rayuwamu data al’ummar da za ta biyo bayanmu ta wanzu. Rana ce da ake bikin yara kanana da basu san komai ba, rana ce ta tabbatar da hakokinsu da kuma jinjina gudummawarsu ga tsayuwar gida da al’umma gaba daya.
Ra’ayin wannan jarida shi ne a daidai lokacin da muke bikin ranar yara ta duniya bai kamata mu manta abin da ya shafi kula da jin dadin rayuwar su yaran ba. Idan za a iya tunawa ‘yan shekarun nan ne aka samu karuwar yara da suke garanranba a kan titunan kasar nan ba tare da suna zuwa makaranta ba, wannan kuma abu ne mai matukar tayar da hankali.
Abu ne mai tayar da hankali a halin yanzu yadda yawan yara marasa zuwa makaranta a Nijeriya ke karuwa. Wani rahoton da aka gudanar a kwanan-kwanan nan ya nuna cewa, yara marasa zuwa makaranta ya karu daga yara Miliyan 10.5 zua yara miliyan 18.5 a shekarar 2022. Wannan wata babbar barazana ce ga rayuwar kasar nan gaba daya, wanda hakan yana kawo tarnaki da ci gaban kasa yana kuma kara talauci a tsakanin al’umma.
Abin lura kuma a nan shi ne yawan yaran da ke garanramba basa zuwa makaranta a Nijeriya sun fi yawan al’ummar kasar Norway, Singapore da Cuba. Wannan abin kunya ne kuma bai kamata a bari ya ci gaba da yin haka ba.
A kasar da al’amurran ‘yan ta’adda ya addaba, ‘yan bindiga a yankin arewa ta yamma da arewa ta gabas da kuma yanklin arewa ta tsakiya, yaran da basa zuwa makartanta da ke yawo a titunan kasar nan na iya zama wajewn da ‘yan ta’adda za su samu kayan aiki.
A bayyane abin yake cewa, ilimi shi ne makullin samun ci gaba a rayuwa ta hanyar bsamun ilimi ne ake samun ci gaba da walwala a harkokin yau da kullum. Saboda haka kange yaranmu daga samun cikakke kuma ingantaccen ilimi ba wai dakile hakkin yaran ba ne kadai amma hakan yana kuma nuna tamkar kawo cikas ga ci gaban kasa baki daya.
Muna bayar da shawarar cewa, yakamata gwamnatoci a dukkan matakai su yi maganin matsalolin da shuka shafi talauci bambanci a tsakanin mata da maza da kuma dukkan matsalolin da ke kawo wa cikas a harkokin rayuwarsu.
A ‘yan shekarun da suka gabata Nijeriya ta ga abubuwan tayar da hankali a kana bin da shuka shafi rayuwar yara, kamar sace ‘yan makarantar Chibok da kisan da yarinya Leah Sharibu, da kuma sauran yaran da suka fada hannun ‘yan ta’adda a lokutta daban-daban a fadin tarayyar Nijeriya.
Rahoton Kungiyar Kare Hakkin Dan’adam ya nuna cewa, tun da aka sace ‘yan mata 276 da ‘yan Boko Haram suka yi a makarantar Chibok, zuwa yanzu ‘yan bindiga sun sace yara fiye da 1,500 a makarantu daban daban.
Wadannan ayyukan ta’addanci ba wai yana tayar da hankullan wadanda abin ya shafa kawai ba ne, yana sanya tsoro da razana a cikin zukatan al’umma a sassan Nijeriya.
A kan haka yakamata wadanan su zaburar da gwamnati a kan bukatar samar da cikakken tsaro ga yaranmu a dukkan makarantun tarayyar kasar nan.
Kowanne yaro yana da hakkin ya yi karatu a yanayi mai aminci tare da samar masa da cikakken tsaro. Ya kamata hukuma ta kara kaimi don ganin ba a kai ga sake sace yara a makarantu ba. Tabbatar da haka kuma yana bukatar hadin kai a tsakanin rundunonin tsaronmu, ta yadda za a dakile shirin da suke a kowanne lokaci na kai hari ga makarantunmu.
Hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta UNICEF ta bayar da rahoton cewa, Nijeriya ne ke dauke da mafi yawan yara kanana da aka yi wa aure tun kafin su kosa, rahoton ya kara da cewa, yara ‘yan mata fiye da miliyan 23 ake aurarwa tun suna kanana a Nijeriya.
Idan za a iya tunawa Nijeriya ta sanya hannu a kan dokar kare hakkin yara ta 2023, a halin yanzu kuma jihohi 34 daga cikin jihohi 36 da muke da su suka sanya hannu a kan doka a jihohinsu wanda aka yi maganar ci da gumin yara, yi musu aure da wuri da auren dole.
A ra’ayinmu, matsalolin da ke fuskantar yara na bukatar a hada hannu don kawo karshensa, lamarin ya kuma fara ne da gwamnati, yakamata gwamnati ta samar da issasun kudi da abubuwan da ake bukata wajen samar da ingantaccen ilimi ga yara a dukkan matakai. Da kuma bukatar zuba jari don gyara tare da gina sabbin azuzuwa don yaranmu su samu yanayin da za su yi karatu ba tare da wata tsangwam ba.
A yayin bikin ranar yara a Nijeriya, ya kamata mu kara fahimtar matsalolin da ke hana ruwa gudu wajen samar wa yaranmu rayuwa ta gari, hakan kuma ke haifar da yawan yaran da basa zuwa makaranta sai yawon bara, ya kamata a gaggauta daukar matakin ganin samar da yanayin da yaranmu za su yi karatu a tsanake ba tare da matsala ba.