Wasu lauyoyin tsohon dan wasan Kamaru, Samuel Eto’o, wanda kuma shi ne shugaban hukumar kwallon kafar kasar, sun musanta cewar an sanar da matakan shari’a a kansa.
A wani jawabi daga kamfanin lauyoyin Faransa, Bey & Associes ya yi watsi da zargin da aka yi wa fitaccen tsohon dan kwallon mai shekara 42 da cewar ”Batun zai shafi bata suna”.
- Kazakhstan, Kasa Marar Ruwa Mafi Girma A Duniya, Tana Da Nata Hanyar Shiga Teku
- Gajiya Ce Ta Sa Na Fadi Yayin Tantance Ni A Majalisa — Balarabe
Ya kara da cewar ba a sanar da Eto’o ba cewar an dauki wani mataki ko sanar da shi abin da ya shafi shari’a tun da a ranar Juma’a aka zargi dan wasan da cewar yana fuskantar mataki na shari’a da ya shafi cogen wasa da cewar ‘yansandan Kamaru na tare da takardun da ake zarginsa da yin amfani da matsayinsa domin amfanin kai da cin hanci da wasu zarge-zarge da dama.
Wannan ba shi ne karon farko da Eto’o ke fuskanta kalubale irin haka ba inda ko a makon jiya, wani rukunin mahukuntan wasanni a Kamaru ya aike da budaddiyar wasika ga hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, kan cewar hukumar kwallon kafa ta duniya ta yi gum, duk da tuhume-tumumen da ake yi wa Eto’o da wasu mukarrabansa a hukumar kwallon kafar kasar.
Wadanda suka sa hannu kan wasikar sun hada da babban mamba a kwamitin Fecafoot, Guibai Gatama da mataimakin shugaban kwararrun ‘yan kwallon kafar Kamaru, wadanda ke gabatar da babbar gasar kwallon kafa ta kasar.
An yi zargin cewar tsohon dan wasan na Barcelona da Inter Milan da Chelsea yana tursasa kansa ta hanyar da ba ta dace ba a kujerar shugaban kwallon kafar kasar (Fecafoot).
Wasikar ta kara da cewar lamarin ya zama mai muhimmanci fiye da wanda ya shafi shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya, Luis Rubiales da ‘yar wasa Jenni Hermoso, inda ta kai FIFA ta dakatar da Rubiales kwana 90 da tsara hanyar da aka dauka don ladabtar da shi.
Lokacin da yake mayar da martani kan wasikar kamfanin lauyoyi na Bey & Associes ya ce Eto’o ya yi tsare-tsare da yawa don sauya alkiblar hukumar kwallon kafar Kamaru da gudanar da mulkin da masu ruwa da tsaki suka mara wa baya.
Sun kuma kira wasikar da cewar mai hadari da bata suna, ya kara da cewar Eto’o ya bugi kirjin tsari da zai kawo karshen wasu daidaiku, wadanda koda yaushe a shirye suke su yi duk abin da zai sa kada su rasa cin hanci da rashawa da suke karba.
A watan Yuni, wani rukunin kungiyoyi ‘yan dagaji da ake kira Amateur clubs a Kamaru suka yi kira da Eto’o ya yi murabus da cewar ya kawo rashin bin tsari, inda suka kada kuri’a da mutum 11-1 suka bukaci da ya kara gaba.
A watan Agusta hukumar kwallon kafar Afirka, Caf ta fara wani bincike kan zargin da ake yi wa Eto’o da cewar ta karbi wasiku daga bangaren masu ruwa da tsaki a kwallon kafar Kamaru, za kuma ta duba dukkan korafin kan doka da ca’ar CAF.
Jawabin na CAF ya kara da cewar zargin yana da girma, amma Eto bai da laifi har sai wata kotu ta tabbar da zargin da ake yi masa.
Lokacin da Eto’o ke kan ganiya an nada shi fitatcen dan kwallon Afirka karo hudu, wanda ya lashe Champions League uku da buga wa Kamaru wasa 115 da lashe kofin nahiyar Afirka biyu tare da kasar wadda ake kira “Indomitable Lions”.