Ranar 5 ga watan Yuni ita ce ranar Muhalli ta Duniya. Ta hanyar kare muhalli ne kawai za mu iya kula da gidanmu wato duniyarmu, hakan ya kasance ra’ayi daya da dukkan bil Adama suka cimma. Ta yaya za a daidaita dangantakar dake tsakanin kiyaye muhalli da kuma ci gaban tattalin arziki da zamantakewa? Kasashen duniya suna binciko hanyoyi daban daban.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da manufar samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, wadda ta zama muhimmiyar ka’ida ga kasar Sin wajen kafa sabon tsarin ci gaba a sabon zamani.
Abin da ake kira “Samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba” a cikin kalaman Xi yana nufin cewa, bunkasuwar tattalin arziki bai dogara ne kan karuwar GDP kawai ba, dole ne a kula da dangantakar dake tsakanin bunkasuwar tattalin arziki da kuma kare muhalli yadda ya kamata, da kuma kafa ra’ayin cewa, kare yanayin muhalli shi ne kyautata karfin samar da kayayyaki, kyautata yanayin muhalli shi ne raya karfin samar da kayayyaki. Ba za a taba sadaukar da muhalli don samun ci gaban tattalin arziki na wucin gadi ba.
Alkaluma sun nuna cewa, fadin yankunan bishiyoyin da kasar Sin ta dasa ya zama na farko a duniya, kuma Sin kasa ce da ta fi saurin karuwar albarkatun gandun daji mafi yawa a duniya. Matsakaicin karuwar yawan makamashin da kasar Sin take amfani da shi a shekara-shekara ya kai 3%, amma matsakaicin karuwar tattalin arzikinta ya wuce 6% a kowace shekara, kuma yawan makamashin da take amfani ya ragu da 26.4%. Kasar Sin ta zama daya daga cikin kasashen da aka fi samun saurin raguwar makamashin da ake amfani da shi a duniya. A shekarar 2023, saurin karuwar wutar lantarki da kasar Sin ta samu daga makamashin da ake iya sabuntawa, alal misali hasken rana da iska, ya fi na baki dayan kasashen G7 yawa fiye da sau hudu, kuma ya ninka fiye da sau biyu idan aka kwatanta da na sauran kasashen duniya baki daya.
Achim Steiner, shugaban hukumar kula da shirin raya kasashe ta MDD wato UNDP, ya bayyana cewa, “Muna son samun ci gaba ba tare da fitar da yawan hayakin iskar Carbon mai dumama yanayi da kuma gurbata muhalli ba, wanda zai kunshi kowa. Kasar Sin ta baiwa kanta wata dama a wannan fannin, har ma ta ba duniya wata damar kara fahimtar yadda za a raya tattalin arzikin duniya ba tare da gurbata muhalli ba.”