ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, November 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Samun Bunkasuwa Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba

by CGTN Hausa
2 years ago
Bunkasuwa

Ranar 5 ga watan Yuni ita ce ranar Muhalli ta Duniya. Ta hanyar kare muhalli ne kawai za mu iya kula da gidanmu wato duniyarmu, hakan ya kasance ra’ayi daya da dukkan bil Adama suka cimma. Ta yaya za a daidaita dangantakar dake tsakanin kiyaye muhalli da kuma ci gaban tattalin arziki da zamantakewa? Kasashen duniya suna binciko hanyoyi daban daban.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da manufar samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, wadda ta zama muhimmiyar ka’ida ga kasar Sin wajen kafa sabon tsarin ci gaba a sabon zamani.
Abin da ake kira “Samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba” a cikin kalaman Xi yana nufin cewa, bunkasuwar tattalin arziki bai dogara ne kan karuwar GDP kawai ba, dole ne a kula da dangantakar dake tsakanin bunkasuwar tattalin arziki da kuma kare muhalli yadda ya kamata, da kuma kafa ra’ayin cewa, kare yanayin muhalli shi ne kyautata karfin samar da kayayyaki, kyautata yanayin muhalli shi ne raya karfin samar da kayayyaki. Ba za a taba sadaukar da muhalli don samun ci gaban tattalin arziki na wucin gadi ba.

  • Kasar Sin Na Hada Kai Da Kasa Da Kasa A Kokarin Inganta Muhallin Halittun Duniya

ADVERTISEMENT

Alkaluma sun nuna cewa, fadin yankunan bishiyoyin da kasar Sin ta dasa ya zama na farko a duniya, kuma Sin kasa ce da ta fi saurin karuwar albarkatun gandun daji mafi yawa a duniya. Matsakaicin karuwar yawan makamashin da kasar Sin take amfani da shi a shekara-shekara ya kai 3%, amma matsakaicin karuwar tattalin arzikinta ya wuce 6% a kowace shekara, kuma yawan makamashin da take amfani ya ragu da 26.4%. Kasar Sin ta zama daya daga cikin kasashen da aka fi samun saurin raguwar makamashin da ake amfani da shi a duniya. A shekarar 2023, saurin karuwar wutar lantarki da kasar Sin ta samu daga makamashin da ake iya sabuntawa, alal misali hasken rana da iska, ya fi na baki dayan kasashen G7 yawa fiye da sau hudu, kuma ya ninka fiye da sau biyu idan aka kwatanta da na sauran kasashen duniya baki daya.

Achim Steiner, shugaban hukumar kula da shirin raya kasashe ta MDD wato UNDP, ya bayyana cewa, “Muna son samun ci gaba ba tare da fitar da yawan hayakin iskar Carbon mai dumama yanayi da kuma gurbata muhalli ba, wanda zai kunshi kowa. Kasar Sin ta baiwa kanta wata dama a wannan fannin, har ma ta ba duniya wata damar kara fahimtar yadda za a raya tattalin arzikin duniya ba tare da gurbata muhalli ba.”

LABARAI MASU NASABA

Sin Za Ta Bunkasa Alaka Mai Inganci Da Dorewa Tsakaninta Da Birtaniya Ba Tare Da Tangarda Ba

Hadin Gwiwar Binciken Sararin Samaniya Mai Kunshe Da ’Yan Sama Jannatin Sin Da Kasashen Waje Ya Shiga Sabon Mataki

CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

    Likitocin Sin Za Su Gudanar Da Aikin Yanar Ido Kyauta Ga Kimanin Mutane 350 A Benin
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Mataimakin Firaministan Sin Ya Gana Da Ministan Wajen Netherlands
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Za Ta Bunkasa Alaka Mai Inganci Da Dorewa Tsakaninta Da Birtaniya Ba Tare Da Tangarda Ba
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Bunkasa Alaka Mai Inganci Da Dorewa Tsakaninta Da Birtaniya Ba Tare Da Tangarda Ba

November 25, 2026
Hadin Gwiwar Binciken Sararin Samaniya Mai Kunshe Da ’Yan Sama Jannatin Sin Da Kasashen Waje Ya Shiga Sabon Mataki
Daga Birnin Sin

Hadin Gwiwar Binciken Sararin Samaniya Mai Kunshe Da ’Yan Sama Jannatin Sin Da Kasashen Waje Ya Shiga Sabon Mataki

November 25, 2026
Likitocin Sin Za Su Gudanar Da Aikin Yanar Ido Kyauta Ga Kimanin Mutane 350 A Benin
Daga Birnin Sin

Likitocin Sin Za Su Gudanar Da Aikin Yanar Ido Kyauta Ga Kimanin Mutane 350 A Benin

November 25, 2026
Next Post
Kungiyar Kwadago Na Shirin Yin Watsi Da Kari Kadan Kan 60,000 A Kan Mafi Ƙarancin Albashi 

Kungiyar Kwadago Na Shirin Yin Watsi Da Kari Kadan Kan 60,000 A Kan Mafi Ƙarancin Albashi 

LABARAI MASU NASABA

Sin Za Ta Bunkasa Alaka Mai Inganci Da Dorewa Tsakaninta Da Birtaniya Ba Tare Da Tangarda Ba

Sin Za Ta Bunkasa Alaka Mai Inganci Da Dorewa Tsakaninta Da Birtaniya Ba Tare Da Tangarda Ba

November 25, 2026
Maryam Golden

NDC Ta Zargi APC Da Daukar Nauyin Hari Kan Maryam Golden A Kano

November 25, 2026
Gwamnatin Tinubu Ta Talautar Da Kowa A Nijeriya — Obi

Gwamnatin Tinubu Ta Talautar Da Kowa A Nijeriya — Obi

November 25, 2026
Hadin Gwiwar Binciken Sararin Samaniya Mai Kunshe Da ’Yan Sama Jannatin Sin Da Kasashen Waje Ya Shiga Sabon Mataki

Hadin Gwiwar Binciken Sararin Samaniya Mai Kunshe Da ’Yan Sama Jannatin Sin Da Kasashen Waje Ya Shiga Sabon Mataki

November 25, 2026
2027: NDC Ta Yi Zargin Ana Shirin Tilasta Wa Obi Janyewa Daga Takarar Shugaban Ƙasa

2027: NDC Ta Yi Zargin Ana Shirin Tilasta Wa Obi Janyewa Daga Takarar Shugaban Ƙasa

November 25, 2026
Mataimakin Firaministan Sin Ya Gana Da Ministan Wajen Netherlands

Mataimakin Firaministan Sin Ya Gana Da Ministan Wajen Netherlands

November 25, 2026
Likitocin Sin Za Su Gudanar Da Aikin Yanar Ido Kyauta Ga Kimanin Mutane 350 A Benin

Likitocin Sin Za Su Gudanar Da Aikin Yanar Ido Kyauta Ga Kimanin Mutane 350 A Benin

November 25, 2026
TUSCOF Ta Yaba Wa Uba Sani Kan Rabon Motoci 39 Ga Ƙungiyoyin Addinai

TUSCOF Ta Yaba Wa Uba Sani Kan Rabon Motoci 39 Ga Ƙungiyoyin Addinai

November 25, 2026
Shugabannin Sin Da Pakistan Sun Taya Juna Murna Game Da Aikin Binciken Sararin Samaniya Na Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashensu

Shugabannin Sin Da Pakistan Sun Taya Juna Murna Game Da Aikin Binciken Sararin Samaniya Na Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashensu

November 25, 2026
 Saraki Zai Jagoranci Kwamitin Gyara Jam’iyyar PDP 

Saraki Ya Nemi Gwamna Abdulrazaq Ya Bar Sarakuna Su Riƙa Karɓar Baƙuncin ’Yan Jam’iyyun Adawa

November 25, 2026

© 2026 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2026 Leadership Media Group - All Right Reserved.