• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

San Francisco Sabon Mafarin Hadin Gwiwar Sin Da Amurka Ne

by CGTN Hausa
2 years ago
Francisco

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden, sun yi musayar ra’ayoyi mai zurfi, a rukunin gidajen alfarma na Filoli dake birnin San Francisco na kasar Amurka ranar Laraba. Taron kolin da aka dade ana jira, na zuwa ne shekara guda bayan ganawar shugabannin biyu a tsibirin Bali na kasar Indonesia.

A jawabinsa yayin ganawar shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin ta dukufa wajen samun daidaito, da dorewar dangantakar lumana da kasar Amurka. A lokaci guda kuma, kasar Sin tana da moriya da ka’idojin da suka kamata a kiyaye, da jan layin da ba za a iya ketarewa ba.

  • San Francisco Sabon Mafarin Hadin Gwiwar Sin Da Amurka Ne
  • Ka Hakura Da Zuwa Kotun Koli, Ka Jira 2027 – Musa Iliyasu Ga Abba

Kasar Sin na fatan kasashen biyu za su kasance abokan hulda masu mutunta juna da zaman tare cikin lumana. Taron dai ya kasance wani muhimmin zabi mai muhimmanci ga kasar Sin, don daidaita dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma halin da ake ciki a duniya.

Masanin tattalin arziki na kasar Amurka Jeffrey Sachs ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ra’ayin mutunta juna, da yin hadin gwiwa,da tattaunawa, da warware matsaloli tare, akwai “hikima sosai”, a cikinsa kuma yana da matukar muhimmanci.

Yana mai cewa, hadin gwiwar Sin da Amurka ba wai kawai kan muradun bai daya ne na kasashen biyu ba, yana kuma nuni da wani nauyi da ya rataya a wuyan kasashen duniya. A yayin taron, shugaba Xi ya yi kira ga kasashen biyu, da su hada kai a matsayinsu na manyan kasashe, yana mai jaddada cewa, za a iya magance matsalolin da ke addabar bil-Adama ne kawai ta hanyar hadin gwiwa tsakanin manyan kasashe.

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

Yarjejeniyar da aka cimma a yayin taron na San Francisco, ta nuna cewa, kasashen biyu suna da moriyar bai daya, kuma za su iya yin hadin gwiwa don samun sakamako mai tarin yawa. Dangantakar Sin da Amurka mai dorewa ba tunanin fata ba ne. Don haka, ya bukaci kasashen biyu su yi aiki tare. Kuma tattaunawa shi ne mataki na farko na amincewa da juna, da mutunta juna da kuma hada kai. Daga Bali zuwa San Francisco, babban jirgin ruwa na hadin gwiwar kasashen Sin da Amurka, ya yi tattaki ta cikin duwatsun teku da kadawar igiyar ruwa. Amma ba a San Francisco za a tsaya ba.

Birnin, wanda ya shaida tarihin musanya tsakanin Sinawa da Amurkawa na tsawon karni, wani sabon mafari ne na dangantakar kasashen Sin da Amurka. (Ibrahim)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi
Daga Birnin Sin

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

October 16, 2025
Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori
Daga Birnin Sin

Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

October 16, 2025
Next Post
Zargin Yaudara: Wani Tela Ya Kashe Tsohuwar Masoyiyarsa A Kaduna

'Yansanda Sun Cafke Malamin Addini Da Sassan Mutum Danye A Oyo

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025
Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

October 16, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

October 16, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

October 16, 2025
Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.