HINDATU SULAIMAN, budurwa ce da ta tsani rokon wani abu a hannun wani ko da iyaye ne kuwa, don haka ta ce ta rungumi kasuwanci domin neman na kashin kanta. A wannan tattaunawar ta yi bayanai masu gamsarwa wadda suka kamata kowace budurwa mai neman kare mutuncin kanta dangane da abin duniya, ta karanta. A karanta hirar har karshe kamar haka:
Da farko za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki
Sunana Hindatu Sulaiman amma anfi kirana da Ummi. Na yi makarantar primary a Aonullah Model School, Ijebu-Ode Ogun State knn. Na yi ‘Secondary school’ guda biya a nan Jihar Ogun mai suna ‘Oke-Eri Comprehensibe High School’. Ina karatun Jami’a a jihar Sakkwaro wato ‘Sokoto State Unibersity’ ina karanta ilimin kwayoyin halittu wato (Microbiology).
Shin Hindatu matar aure ce?
A, a ni ba matar aure bace
Malam Hindatu ‘yar kasuwa ce ko kuwa karatu kade tasa a gaba?
Eh to ana iya cewa ‘yar kasuwa nake, saboda gaskiya ina dan taba kasuwanci kadan kadan haka de ba lefi.
Wannen irin kasuwaci kike yi?
‘Company Business’ nake yi ma’ana zaka yi ‘Ordering’ wato abin da ake nufi da ‘order’ shi ne za a tura maka kaya a hoto ka gani idan ya myi aka sai ka biya kudinsa sannan na cire ribata sai na tura kamfani aiko maka da kayanka wato ni zan saro maka daga kamfani.
Shin me kasuwancin naki ya kunsa? Ma’ana kamar me da me kike sarowa?
Ina sayar da kayan kwalliya na mata (Cosmetics), Turare na mata da maza sai kuma ‘Skincare Creams for both Ladies and Gentlemen’, wato man gyaran fata na maza da mata.
Me ya je hankalinki har kika shiga wannan kasuwanci?
Abin da ya ja hankali na shi ne ni mutum ce da ban son ina yawan tambayar Babana abu, shi yasa na ce nima ya kamata na fara Kasuwanci.
Hindatu baki fada mana matakin karatunki ba?
Ina Jami’a ne yanzu aji na biyu wato ‘200 lebel’.
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?
Da yawa, misali kayan da muke sayarwa gaskiya suna da tsada, idan ba wanda ya taba ko yana jin ana maganar ‘Products’ din ba ba zai iya saya ba. Shi yasa wani lokaci ake kashe maka kwarin gwiwa.
Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika cimma a harkar sana’ar?
Ban cimma ba amman InshaAllah na san ina kan hanya nan bada jumawa ba.
A da can da kike karama mene ne burinki?
Burina shi ne na zama Likita
Wanne abu ne yafi faranta miki rai game da sana’arki?
Yadda nake ganin anawa wasu yadda nake gani ana bawa mutane kyaututtua wanda ya shafi (Awards) a kana bin da suke sayarwa, ina jin dadin hakan, shi ya sa nake sa a raina nima lokaci zai zo da za a karrama ni a kan wannan sana’ar.
Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?
Hanyar da dama, ina tallata sana’ata ta yanar gizo wato (By posting in all my social handles).
Dame kike so mutane su rinka tunawa dake?
So nake su gwada sayan kayana wato ‘Pproducts’ dina nasan za su ji dadin shi, to daga nan na san kuma za su rinka tunawa dani.
Ga karatu ga kuma hidimar sana’a shin, ta yaya kike hadasu?
Na riga na saba da wahalar makaranta don haka wahalar kasuwanci ba komai ba ne a gare ni
Wanne irin addu’a ne idan aka yi miki kike jin dadin?
Allah yasa ki ci amfanin wahalar ki, ina yawan jin wannan addu’ar ina jin dadin addu’ar nan.
Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyayanki?
Gaskiya ina samun goyon baya musamman ma daga wajen Umma na, amman gaskiya dukkan su biyun na ba ni goyon baya dari bisa dari.
Kawaye fa?
Gaskiya ba ni da aminiya sai dai ina da kawaye da yawa kowa nawa ne
Me kika fi so cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Na fi son dogowar riga ko riga da siket da hijab. Ni bana kwalliya.
A karshe wanne irin shawara za ki ba ‘yanuwanki mata?
Shawarata shi ne mu tashi tsaye su nemi sana’a don sana’a shi ne rufin asirin mace.