Kamar kullum dai! Shafin Taskira ya kan zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma, wadanda suka hadar da Zamantakewa na rayuwar yau da kullum, Zaman aure, Rayuwar Matasa, soyayya, da dai sauransu. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda karamar Sana’a ta fi Maula, sau da dama matasa na samun kananan sana’o’in wani sa’in ma cikinsu har da masu gwabi, sai dai kuma su matasan sukan kalli wannan sana’a a kaskance, tare da kallon sun fi karfinta, wanda hakan ya kan kai da sun rasa abin yi, karshe a bige da Maula. Ko ta wacce hanya za a wayar da kan matsa game da karamar Sana’a ta fi Maula?, Wadanne irin sana’o’i ne kanana wadanda za su taimakawa mutum muddin ya ruke sana’ar?. Wannan ya sa shafin Taskira ya ji ta bakin mabiya shafin game da wannan batu, ga kuma ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Zulkifilu Lawal (Naka Sai Naka):
Hanyar da za a wayar da kan matasa cewa karamar sana’a ta fi  maula ita ce; Nuna musu sanin mutuncin kai da sanin ya kamata tare da fadamasu amfanin sana’a da kuma ribar da ake samu a cikinta, in har kana da sana’a ka fi mutunci a idon mutane, idan kana da sana’a za ka taimaki kanka da wasu masu kananan bukatu irinka. Akwai sana’o’i da yawa wadanda idan ka rikesu za su taimaki rayuwarka kamar sana’ar Dinki, Kira, Hada takalmi, Kafinta, Walda, Rini, Gyaran Waya, Wanki da Guga da suransu. Shawara ita ce; duk irin sana’ar da ka tsinci kanka a cikinta ko ta gado ce ko kuma wadda ka koya ka rike ta da mutunci domin duk abun da ka dauka da mutunci za ka ga albarkarsa, ita sana’a ba dole sai kayi kudi da ita ba in har za ta rufa maka asiri ka riketa da muhimmanci gwargwadon yadda ka rike abu da muhimmanci, gwargwadon yadda za ka ga alkairinsa, Allah ya sa mu dace Amin.
Sunana Usman Abdullahi:
Wannan magana haka take karamar sana’an ta fi maula, saboda shi maula yana sa mutuwar zuciya da rashin yin tunanin neman abin yi. Muna da sana’o’i masu yawa a kasar hausa, kamar; Sassaka da Rini da sayar da Nama. Raina sana’a yana daya daga abin da ya ke sa samari har ma da ‘yan mata sata da kwace da dai sauransu, Allah ya ba mu ikon neman na kan mu, ya sa mu fi karfin nema a wajen wani.
Sunana Auwlu Abdullahi Umar Kiru:
Sana’a:- Ita ce hanyar da mutum zai bi domin ya tsaya da kafarsa, ko kuma hanya ce da dan Adam zai bi domin dogaro da kansa ta nayin saye da siyarwa ko ta hanyar yin wani abu don a biya shi. Karamar Sana’a tafi maula nesa ba kusa ba!. Rungumar wata hanya wacce da kudi kalilan ko kuma wata basira da mutum zai iya amfani da ita domin ya samu abin dogaro da kansa har ma ya taimkawa wasu da suke a kewaye da shi. Duk sana’ar da bata bukatar makudan kudi ko ilmi mai zurfi za mu iya cewa ko mu kira ta da suna karamar sana’a. Duk lokacin da mutum ya yarda ko ya yi imani da duk wata hanya zai samu abin biyan bukata ta yau da kulum ba tare da maula ko dogaro da wani ba, a wannan yanayi babu wani ko wata da zai iya yi maka kallon banza ko kallon kaskanci domin ya san kasan mutuncinka ko darajar da Allah (SWA) ya yi maka.
Ita maula a addinimmu na musulinci haramun ce, sannan kuma al’adar mu na Hausa su ma sun kyamace ta mutuka. Kananan sana’o’i sun kasu kashi biyu; Karamar sana’a wacce ke bukatar kudi kalilan, kamar su: Sayar da rake, Sayar da shayi, Sayar da ruwa (pure wata), POS/Changing waya, Sayar da kayan kamshi/kayan shayi, Sayar da biredi, ‘Frozen chicken/ eggs
Business centre/cafe’ da dai sauransu. Sana’o’in da basa bukatar kudi kafin farawa, ma’ana suna bukata iya wa da lafiya. Gini, Gyaran wuta da ‘satellites’, Dillancin filaye da gida ce, Noma da kiwo, Faci. Duk mutumin da Allah ya albarka ce shi da karamar sana’a ya wofuntar da ita hakan ba abu ne mai bullewa ba, wanda hakan zai sa ayi nadama wacce ba za ta musaltu ba. Shawara zuwa ga yanuwa; 1.Mutuncika ne zai dore ta wannan sana’ar, 2.Rukon iyalai da ‘yan uwa, Samun farin ciki, Alfahari da dai sauransu. Rashin daukar shawara; 1.Nadama, 2. Maula, 3.Zubar da kima da mutunci a cikin al’umna, 4 Rashin rike kai da iyali.
Sunana Muhammad Murtada (Bazazzagin Me Iyali) Daga Birnin Zariya:
Maganar gaskiya idan ana so a wayar da kawunan matasa akan karamar sana’a sai an yi daya cikin wadannan abubuwan ko ma baki daya: Na farko:sai wadannan masu kananan sana’o’in sun rika jawo matasa a jiki suna nuna masu mahimmanci da amfanin da wannan sana’ar da suke ciki. Na biyu: sai masu wannan kananan sana’o’in sun cire mugunta da keta da nuna bambanci tsakanin na su da wanda ba na suba. Na uku; Sai mutane sun daina nuna kyama akan masu kananan sana’o’in. Na karshe: wadannan masu kananan sana’o’in sun rika nuna soyayya da tausayawa akan wadanda suke karkashin su hakane zai sa ma da sauran matasa kaunar kananan sana’o’in. Akwai sana’o’i kamar su Dinkin hannu ko na keke, acaba, fawa, Bumburutu dadai sauransu. Maganar gaskiya ba daidai bane ace amatsayin ka na matashi musamman kuma ace É—an makaranta me buri ace kasami damar yin É—ayan biyun waÉ—annan sana’o’in amma ka wofintar domin hakan kuskure ne babba, ko da’ce ma ba kayin É—aya daga cikin waÉ—annan Æ™ananan sana’o’in ya kama ta kayima kanka karatun ta natsu kayi maza ka kama sana’a musamman a wannan lokacin da muke ciki domin Æ™aramar sana’a ta fi Maula.
Sunana Abba Gada Rano Unguwar Liman Gada:
Gaskiya akwai hanyoyi da dama, duba da yadda muka tsinci kanmu a Nijeriya yanzu ba a bawa mutum shawara ya ma fara sana’a, duba da yadda kasar take ciki, su kansu wadanda ake yi wa maular ta kansu suke. A shayi da biredi (Wanda jarinsa bai huce 5000), Siyar da katin waya da Data (wanda jarinsa bai wuce 10000. Ruwan Leda ‘Pure water’. Gaskiya a halin yanzu masu karamar Sana’a wallahi in dai za su rike to tafi ma’aikacin da yake mataki na 8 mai digiri ne, indai za ka samu ribar dubu uku a rana.
Sunana Fatima Sunusi Rabi’u Marubuciya daga Jihar Kaduna:
Ina kira ga matasa mu tashi tsaye domin ganin mun rike sana’armu komai kankantar ta, domin idan kana nema ka fi karfin maula, me ma zai kai ka? Allah ya raba mu da mutuwar zuciya, Allah ka wadata mu da wadatar zuciya mu fi karfin maula, koya ka ke juya sana’a ka fi karfin ka ce a baka. Matasa maza da mata akwai sana’o’i a kasar Hausa daban-daban da ya kamata ka rike, idan ma karatu ka ke za ka iya yi, haka ka kammala baka samu aiki ba ka rike sana’a da kyau domin ka wucewa ba ni-ba ni. Akwa; Kafinta ko Walda ko Tela, duk wanda ka rike a ciki za ka ci abinci har ma ka yi wa wani, kai maza har sai da ‘brush’ da su kum, abin sosa kunne, su hodar yara da sauransu idan har za ka rike wannan ka fi karfin maula. Mata sana’ar gida za ki iya; Dinki idan kin iya ko Saka, Akwai yin su; Illoka, Tuwan madara, Gullisuwa, kai mata fa akwai sana’a kanana da yawa wanda idan kin iya to kin wuce ‘yar murya ko jiran wani ya baki. Wallahi su bi a sannu, domin irinsu ne ‘yan maula, kana gani wallahi naira goma sai ta gagareka, ka rike sana’arka komai kankatarka, ko ganin mutuncinka an fi. Amma kai kenan kullum zaman saman benci ko bin inuwa da wannan ta kare a bi waccen, yunwa cike da ciki sai karyar banza. Ina bawa matasa maza da mata shawarar su rike sana’a komai kankantar ta domin tsira da mutunci, masu iya magana dai suna cewa Ƙwai a baka – Ya fi kaza a akulki haka sana’a sa’a.
Sunana Abbale Isma’el daga Jihar Kano Jogana:
Gaskiya ne to da farko dai da a ce baka ake yi, gara a ce kai ka ke bayarwa, ko da a cikin mutane kafi daraja da kima akan ace maula ka ke yi, kowa abin da ya ke ganinka da shi ko da za a baka, sana’a komai kankantarta za ta rufa maka asiri. Sana’o’i kuma akwai irinsu; Shushaina, Turin ruwa, Yankan farce duk za su taimakawa mutum, to duk wanda ya sami sana’a komai kankantarta ya yi kokari ya jajirce watarana burinsa zai cika, Allah ya sa mu dace.
Sunana Nabeela Dikko daga Jihar Kebbi Nijeriya Garin Argungun Garin Kanta (Ko da mai ka zo an fi ka):
Ai ido mudu ne sannan jiki magayi kamar yadda guntun gatarinka aka ce ya fi sari ka bani, a gaskiya sana’a nasara ce domin ya fi yawon maula, domin komai kankantar sana’a za a dogara da kai da ita, sannan da sannu sai ta kai mutum a inda bai yi tsammani ba. Maula ba kyau yana sanya mutuwar zuciya, yana kawo wulakanci da raini, don haka matasa a rinka sana’a ko don a huce takaicin zamani. Maza da mata matasa akwai sana’oi da dama kamar su; Wanki, Guga, Dako, sayar da Rake, Aya, da sauransu, mata aÆ™wai su Alale, Awara, Kunun Zagi su Zobo, Ruwa da sauran su, duk sana’a idan mutum ya rike ta za ta iya taimaka ma shi. Ai duk wanda ke raina sana’a yana ji ya kuma gani watarana abin da ya fi karfi zai gagare shi, don haka duk sana’ar da mutum ya samu mai kyau wacce addini ya yarda da ita ya kama don ya fi zaman banza.
Sunana Habiba Mustapha Abdullahi:
A gaskiya komai kankantar sana’a ta fi ka je wajen wani ka roka ko ba komai in ka tafi kila a rana ya fadawa mutum uku, su ma su fadawa mutum uku, to me ne amfanin irin wannan?, Maula tana sa a raina mutum koda yana da girma ko aure. Muna da sana’o’i kamar Wanki da Guga, Tukin Napep, saida kayan wasan yara da dai sauransu. Maza da mata dan Allah mu yi kokarin rike sana’a komai kankantar ta ta fi Maula, a gida wani ko kan titti ba shi da amfani, kai ma da za a bawa ranka a bace wanda zai baka na shi ran ma a bace, saboda wani maular ma ba shi da amfani ko wa ya nemi na shi shi ne hasken zuciya da farin ciki idanu Allah ya sa mu dace.
Sunana Musbahu Muhammad Gorondutse Kano:
Idan sun yi Maular ko rokon ka da a basu abin da suka roka. Sana’ar hannu kamar Dinki, Kafinta, Aikin Gini da kuma ‘Online Business’, tunda ana yinsa babu ko sisi sai dai ‘Mobile Data’ kawai. Matasa su gane cewa duk kankantar sana’a ta fi Maula kuma Allah zai iya daukaka mutum da karamar sana’a ya bashi kudi masu yawa ta sanadiyyar sana’ar.