Salamu alaikum, barkanmu da sake saduwa wannan mako a shafinmu mai albarka inda za mu yi magana a kan yadda ake dinki.
Sana’ar dinki sana’a ce da mutane ke yi wanda suke dinka tufafin da mutane suke sawa, yawanci mutum zai kai wa wanda ake kira tela shi ne wanda ya dauki sana’ar dinki a matsayin hanyar samun kudinsa, za a kai mashi yadi, shadda ko kuma wata atamfa ya dinka masa zuwa wani lokaci ya amsa bayan ya biya shi.
Sana’ar dinki sana’a ce da ake samun kudi sosai saboda mutane da dama masu wannan sana’a sun zama masu kudi,sun tara dukiya sosai, don sana’a ce da za ka ji ana cewa wannan azumin na tara dubu dari biyu ko fiye da haka musamman lokacin bukukuwa kamar Sallah da sauransu.
Musamman a wannan zamanin da za ka ga styles na dinki daban daban wanda kullum kara gyara al’adun Hausawa suke da haska su, kowa yana sha’awar ya dauki wanka
Yadda za ka fara dinki:
Na farko jarin sayen kayan aiki:kowacce sana’a na bukatar jari ko yaya take kafin fara samun kudi da ita, ya danganta karami ne ko babba, kuma wannan sana’a kana iya fara ta da karamin jari kawai dai abubuwan da kake bukata su ne ya kasance ka sayi duk wani karamin kayan ma’aikaci ko kuma babba yadda da ko ka fara aiki kawai ci gaba za ka yi.
Kayan da ake bukata manya da kanana, ana bukatar kayayyaki kamar haka:
Keken dinki, zare, allura, almakashi, reza, man keken dinki, abin awo (tape) sauran engina kamar na ziza idan da daman hakan, koyon sana’ar kusan dukkan sana’oin hannu ka na da bukatar ka koye shi in dai kana so ka yi zarra.
Akwai wurare da dama da za ka koyi wannan sana’a wanda suka hada da wajen horaswa na sana’o’in zamanin na garinku ko kuma ka samu kudin ka kalilan ka je gun mai shago ka biya shi lada mishi ya koya maka. Abubuwan bukata yayi koya:
Karangar nama saboda koyon yadda ake yanka yan kyallaye yadda in ka fara iyawa za ka dan dinka kayan aiki a lokacin da ka je da kayan aikin ka domin koyon wannan sana’ar ka sa ma ranka cewa za ka tsaya ka natsu ka fahimci yadda ake yanka ka tabbatar ka iya domin shi ne za ka iya sarrafa design kala-kala da za ka ja hankali masu kawo maka dinki.
Bayan ka dawo gida kuma ka ci gaba da kokarin yawan maimaita abun da aka koya maka kana kara yin sa a aikace yadda ba za ka yi saurin mantawa da shi ba
Sai kuma ka sawa kanka hakuri don hakuri shi zai kai ka ga cimma buri.
Allah ya taimaka.