Game da sanarwar matsin lamba a fannin tattalin arziki, wadda kasashen Amurka, da Birtaniya, da wasu kasashe suka fitar tare, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Amurka ce ta yi kira ga membobin kungiyar kawancen “Five Eyes” da kasar Japan, da su fitar da wannan sanarwa, to sai dai kuma abubuwan dake cikin sanarwar na nuni ne ga irin laifukan da Amurka ta ke aikatawa.
Wang Wenbin wanda ya yi wannan tsokaci a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Litinin, ya ce Amurka ta gabatar da dokar mattarar bayanai ta microchip, da kimiyyar wannan fanni, inda ta hana kamfanonin da suka karbi rancen kudin da gwamnatin Amurka ta ba su, su kara samar da mattarar bayanan ta microchip ga kasar Sin a cikin shekaru 10, da yin matsin lamba ga kasashe membobin kawancenta, da su kayyade fitar da sassan na’urorin laturoni na semiconductor ga kasar Sin, kuma kowa dai ya san hakan matsin lamba ne a fannin tattalin arziki.
Kaza lika Amurka ta yi bayani game da tsaron kasa daga bangare daya, da yin amfani da karfinta wajen yin matsin lamba ga kamfanin Huawei, da TikTok da sauransu, wanda hakan ba manufar kasuwanci ba ce.
Bugu da kari, Amurka ta kawo cikas ga zaben alkalin hukumar gabatar da kara na kungiyar kasuwanci ta duniya WTO, a shekaru da dama da suka gabata, lamarin da ya haddasa dakatar da tsarin daidaita matsaloli, baya ga haka, ba ta aiwatar da hukuncin da WTO ta yanke ba, wanda hakan ya haifar da babbar barazana ga tsarin ciniki a tsakanin bangarori daban daban.
Wang Wenbin ya jaddada cewa, Amurka tana aiwatar da mugun aiki a fannin tattalin arziki da cinikayya, da kuma dora alhakin hakan kan wasu kasashe, ta yadda hakan ya samar wa sauran sassa damar gano hakikanin yanayin Amurka, wato kawo illa ga ka’idojin tattalin arziki, kasuwanci da ka’idojin ciniki na duniya. (Zainab)