Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin, ya ce tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kawo hadin kai a jam’iyyar APC.
Ganduje ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa ne a ranar 3 ga watan Agusta, 2023, yayin taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar (NWC) da aka gudanar a Abuja.
- Kirsimeti: Gwamnatin Kebbi Ta Raba Shinkafa Don Tallafa Wa Kiristoci
- ‘Yan Bindiga Sun Ƙwace Kayan Abincin Kirsimeti A Kaduna
Sanata Barau a wani sako da ya aikewa Ganduje a ranar bikin cikarsa shekaru 75 da haihuwa ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya ce, Ganduje ya jagoranci jam’iyyar zuwa nasara a zaben gwamnonin jihohin Edo, Ondo, Kogi da kuma Imo.
Don haka, Sanata Barau ya nemi Ganduje da ya kara azama wajen lashe sauran jihohin da suka yi wa jam’iyyar tutsu.