Tsohon Sanatan Kaduna ta kudu kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sanata Ɗanjuma Laa, tare da wasu ‘ƴan jam’iyyar sun fice daga PDP zuwa APC mai mulki.
Yadda ‘Yan Jam’iyyar PDP Suka Koma Jam’iyyar APC A KadunaGwamnan jihar ta Kaduna, Sanata Uba Sani ne ya karɓi sanatan tare da ragowar waɗanda suka koma APC a wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi na jam’iyyar a garin Kafanchan da ke jihar.
Ragowar waɗanda gwamnan ya karba sun haɗa ‘ƴan majalisun tarayya ma su ci da tsofaffi, da ‘ƴan majalisun dokoki na jihar da tsofaffin shugabannin kananan hukumomi da shugabannin jam’iyya da sauransu na jam’iyyun PDP da Labour Party (LP).
‘Ƴan majalisun sun haɗa da mai wakiltar karamar Zangon Kataf da Jaba a majalisar wakilai ta kasa da Hon. Amos Gwamna Magaji da Hon. Donatus Matthew da suke wakiltar Kaura a majalisun wakilai da na dokoki.
Sauran su ne tsohon dan majalisar wakilai Hon. Godfrey Ali Gaiya da ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Jaba a majalisar dokokin jihar Hon. Henry Marah Zakarieh da sauransu.
Gwamna Uba Sani ya godewa shugabannin jam’iyya a jihar bisa kokarin da suke na jawo mutane zuwa jam’iyyar sannan ya sake jaddada aniyar Gwamnatinsa na ci gaba da bijiro da ayyukan alheri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp