Dan Majalisa mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya a majalisar dattijai, Sanata Rufa’i Hanga, ya mayar da martani kan sukar da ake masa dangane da tallafin tukwanen yumbu 2,000 da likafani yadi 10,500 da ya bayar ga makabartar musulmi a mazabarsa.
Da yake magana a wani taron manema labarai, Sanata Hanga ya fayyace cewa, gudummawar wata karamci ce na kashin kansa da nufin mutunta al’adar gidansu, ba wai daya daga cikin ayyukan mazabarsa ba kamar yadda aka yi ta cece-kuce akai.
- Yadda Rikicin ‘Yan Daba Ya Ci Rayukan Mutane 2 A Kano
- NLC Na Gudanar Da Zanga-zanga A Ofishin KEDCO Na Kano Kan Ƙarin Ƙuɗin Wutar Lantarki
Hanga, ya lashe zabe ne a karkashin inuwar jam’iyyar NNPP, kuma yanzu haka, shi ne mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa ta 10, ya jaddada cewa, tallafin da ya bayar, ya yi ne don neman tsira da yardar Ubangiji.
“Wannan tallafin, al’adar gidanmu ce, kuma ina fatan ci gaba da wanzar da ita har karshen rayuwata.” In ji Hanga