Rundunar ‘yansanda a Jihar Kano ta fara gudanar da cikakken bincike game da mutuwar wasu matasa biyu a wani mummunan rikici da ya barke tsakanin wasu kungiyoyin ‘yan daba a Darmanawa Kwatas a ranar Lahadin da ta gabata.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safe, yayin da aka ga wata runduna ta ‘yan daban dauke da muggan makamai suna tafka kazamin fada wanda hakan ya sa ‘yansandan suka yi gaggawar tarwatsasu.
- Bangaren Samar Da Motoci Na Kasar Sin Ya Samu Ci Gaba A Rubu’in Farko Na Bana
- Ɗaliba Ta Maka Makarantarsu A Kotu, Ta Nemi Diyyar Miliyan ₦505 Kan Cin Zarafinta
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, SP Haruna Kiyawa a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce, rikicin ya barke ne a yayin wani bikin Gangi – bikin mafarauta da wani dan shekara 59, Muhammad Barde ya shirya domin murnar bikin auren ‘ya’yansa da za a yi kwanan nan.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Mohammed Usaini Gumel ya bayar da umarnin cafke Barde tare da wasu mutane biyu da yanzu haka suke hannun jami’an ‘yansanda.
Rikicin ya yi sanadin mutuwar Sadiq Abdulkadir, mai shekaru 23, da ke zaune a Darmanawa kwatas, da Muhammad Sani, mai shekaru 22, da ke Sallari kwatas, a Jihar Kano