Sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya a majalisar dattawa ta kasa, Sanata Aminu Iya Abbas, ya jajantawa mutanen da iftila’in guguwar iskar hadarin ruwan sama ta lalata musu gidaje.
Wuraren da iskar ta lalata sun hada da gidaje da wuraren ibada da kuma gine-ginen cibiyoyi a gururuwan Pella, Garari, Wuro Garba, Jabba, Lugga da kuma Mombol a karamar hukumar Hong a jihar Adamawa.
- Bullar Annobar Cutar Kyanda Ta Tilasta Rufe Makarantu A Adamawa
- Mun Kawo Jam’iyyar AAC Ne Domin Al’ummar Adamawa – Doubli
Sanata Abbas wanda shi ne shugaban kwamitin kimiya da fasaha da kire-kere na majalisar dattawan ya kuma yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da su gaggauta samar da kayayyakin agaji ga wadanda guguwar ta shafa akan lokaci.
Dan majalisar tarayyar ya’yi kiran ne a lokacin da yake jajanta wa wadanda abin ya shafa ta ofishin yada labaransa dake Yola, kan bala’in guguwar da ta afku a baya-bayan nan da ta yi sanadiyyar rasa matsugunai da kadarori na miliyoyin naira.
Ya ci gaba da cewa “ana bukatar taimakon gaggawa musamman kayan aikin gini zai taimaka wajen sake gina gidajen al’umman da abin ya shafa.
“Ina kira ga mutanen da abin ya shafa musamman wadanda ke yankunan karkara da su kaurace da kiyaye sare bishiyoyi, domin hana asarar rayuka da dukiyoyi a Irin wannan bala’o’in.
“Ina aiki tare da masu ruwa da tsaki, domin samar da hanyoyin da za’a bi, na ganin hukumar bada agajin gaggawa ta jiha (ADSEMA) da hukumar bada agajin gaggawa ta Kasa (NEMA) da sauran kungiyoyi na gwamnati da na masu zaman kansu, sun kai dauki ga al’ummomin da abin ya shafa” inji Abbas.