Sanata Masud Doguwa, fitaccen ɗan jam’iyyar APC a Jihar Kano, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP. Wannan sauya sheƙar ya zo ne tare da kakkausar suka ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda ya zarge ta da rashin tsari da aiwatar da manufofi masu cutarwa ga al’umma da suka ƙara talaucin jama’a a ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar yana bayyana sauya sheƙarsa, Doguwa ya nuna damuwarsa da rashin amfani da mutane masu gogewa yadda ya kamata da kuma rashin gamsuwa da salon tafiyar APC.
- Da Ma Sai Da Muka Gargadi Ƴan Nijeriya Kan Sake Zaben APC – Tambuwal
- Ranar Dimokuraɗiyyar: Ƴan Nijeriya Fushi Suke, PDP Ga Tinubu
Ya bayyana takaicinsa cewa, duk da yawan ƙwarewar su a siyasa, ba a cika damawa da su a sha’ani ko tarukan jam’iyyar ba don su ba da gudummawar su.
Doguwa ya kuma caccaki manufofin gwamnatin APC, yana mai cewa suna cutar da talakawa. Ya yi zargin cewa manufofin gwamnatin ba su dace da ra’ayin siyasar sa ba, kuma tsarin da APC ta bi ya haifar da ƙarin matsaloli ga talakawa.