Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, wacce aka dakatar tsawon wata shida, na shirin komawa majalisar dattawa a ƙarshen wannan watan. Lauyanta, Barista Victor Giwa, ya bayyana hakan a Abuja inda ya ce Sanatan tana hutu a Landan, amma ta shirya halartar zaman majalisar da za a dawo ranar 23 ga Satumba.
A cewar Giwa, babu wani cikas da zai hana ta ci gaba da aikinta domin shugabancin majalisar ya nuna shirinsa na karɓarta. “Komai ya kammala, dakatarwar ta ƙare, kuma an tabbatar da cewa babu wani shinge daga shugabancin majalisar,” in ji shi.
- Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja
- Natasha Ta Koma Majalisar Dattawa Duk Da Tsaurara Tsaro
Sanata Natasha ta sha cewa dakatar da ita bai rasa nasaba da ƙorafinta kan shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, wanda ta zarga da cin zarafi. Sai dai majalisar ta ce ta dakatar da ita ne bisa rahoton kwamitin ladabtarwa, wanda ya kuma karɓe mata dukkan alfarmar ofis da albashinta.
Koda yake ta samu hukuncin kotu da ya amince da dawo da ita, shugabancin majalisar ya dage cewa dole ta kammala dakatarwar kafin ta dawo. Yunƙurinta na komawa ofis a watan Yuli ya ci tura bayan jami’an tsaro sun hana ta shiga.
Yanzu da dakatarwar ta ƙare, lauyanta ya tabbatar cewa duk wata shari’a ba za ta zama cikas ga dawowarta ba, yana mai cewa “duk sauran shari’o’in za su zama kamar darasi ne kawai a littafin doka.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp