Sanatoci biyu na jam’iyyar PDP, Sanata Mathew Urhogide da Ayo Akinyelure sun fice daga jam’iyyar.
Sanarwar murabus din nasu na kunshe ne a cikin wasu wasiku daban-daban guda biyu da suka aike wa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan kuma aka karanta yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
- Burina Tinubu Ya Tilasta Wa Maza Kara Aure —Rashida Mai Sa’a
- Gwamnan Abba Gida-gida Ya Rushe Duk Nade-nade, Ya Kwace Duk Kadarorin Gwamnati Da Ganduje Ya Sayar
Sanata Urhogide ya wakilci mazabar Edo ta kudu a majalisar dattawa yayin da Sanata Akinyelure ke wakiltar Ondo ta tsakiya.
A cikin wasikar, Sanata Urhogide ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne saboda gazawar jam’iyyar PDP wajen daidaita rikicin jam’iyyar.
Ya ce, “Na ajiye mukamina na jam’iyyar PDP, nan take.
“Wannan matsayar yanke shawara ta samo asali ne daga rikicin siyasa da ke tasowa a halin yanzu daga bambance-bambancen da aka gaza shawo kan su a cikin jam’iyyar PDP a matakin kasa musamman a Jihar Edo.
“Wadannan rigingimu sun kai matakin da suka sa ba zai yiwu wani kamar ni wanda aka tabbatar da dimokuradiyya ya yi aiki da girma kamar yadda na yi hasashe a tafiyar siyasa ta ba.
“Duk da haka ina godiya ga jam’iyyar da ta ba ni damar cimma burin yi wa kasata hidima a matsayin sanata har sau biyu – wanda kwarewa ta ba ni damar yin aiki tare da dukkan abokan aikina.”