Wani bincike daga Jaridar WikkiTimes ta yi ya bayyana cewa sanatoci 12 daga wasu jihohin arewacin Nijeriya ba su gabatar da kowanne ƙudiri ba a cikin watanni 15 na farkon wa’adin majalisar dokoki ta 10, wadda ta fara aiki tun ranar 13 ga Yuni, 2023.
Waɗannan sanatoci na wakiltar yankuna da ke fama da matsaloli masu tsanani irin su rashin tsaro, talauci, rashin ingantaccen ababen more rayuwa, da rashin aikin yi.
- Akwai Bukatar Shugabannin Arewa Su Farka – Sarkin Fawa
- Gwamnatin Tarayya Da Jihohi Sun Kawar Da Fargabar Ɓallewar Madatsun Ruwa A Arewa
Daga cikin Sanatocin da ba su gabatar da ƙudiri ba akwai Abdul Ningi (Bauchi ta tsakiya), Musa Mustapha (Yobe ta Gabas), da Ahmed Lawan (Yobe ta Arewa), wanda shi ne tsohon Shugaban Majalisar Dattawa. Wasu sanatocin kuma sun fito daga jihohin Adamawa, Taraba, Sokoto, da Filato, waɗanda duk suna fama da manyan matsalolin tattalin arziki da zamantakewa.
Duk da matsalolin da ke addabar waɗannan yankuna — kamar rashin ingantaccen kiwon lafiya, ilimi, da ababen cigaban rayuwa — wadannan sanatoci ba su ɗauki matakin samar da doka ba don magance wadannan matsaloli masu tsanani.
Masana sun yi Allah wadai da rashin wannan aiki na ƴan majalisar, suna kallon hakan a matsayin gazawar wakiltar muradun al’ummominsu da kuma ɗumama kujera.