A wani kokari da kungiyar Sanatocin Arewacin Nijeriya ke yi, Kungiyar ta gudanar da wani taro a ranar Talata domin magance matsalolin da suka dabaibaye batun rufe iyakokin kasar da jamhuriyar Nijar da kuma matsalar wutar lantarki sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a baya-bayan nan.
Sanatocin, wadanda suka bayyana damuwarsu, ba tare da wata shakka ba, sun bukaci Nijeriya a karkashin jagorancin kungiyar ECOWAS, da ta dauki matakin gaggawa don sake bude iyakokinta da Nijar tare da maido da ayyukan wutar lantarki. Sun tabbatar da cewa rufewa da katsewar wutar lantarki na yin illa ga rayuwar marasa galihu.
Sanata Lawal Adamu Usman, shi ne ya bayyana hakan bayan zaman ganawar ga manema labarai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp