Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sake jaddada cewa Muhammadu Sanusi II, ne sarkin Kano da doka da kuma al’umma suka amince da shi.
Kwankwaso, ya faɗi haka ne cikin jawabinsa a wajen yaye ɗalibai karo na huɗu na Jami’ar Skyline da ke Kano, inda ya ce duk wani wanda aka naɗa daga wajen jihar ba shi da ikon yin tutiya a idon al’umma da gwamnatin Kano, cewa shi ne sarki, kana ya yaba wa hukumar jami’ar kan jajircewarsu wajen inganta ilimi tare da taya ɗaliban da suka kammala karatu murna, yana mai cewa fiye da kashi 60 cikin 100 na waɗanda suka yi ƙoƙarin kammala karatun mata ne.
Ya shawarci matasa maza su dage wajen karatunsu, tare da gargaɗin cewa kada su din yin sakaci da har mata za su samu damar yi musu zarra a muhimman fannoni na cigaban ƙasa.
Kan batun tsaro kuwa, tsohon gwamnan ya nuna damuwa kan hare-haren da wasu ’yan bindiga ke kaiwa daga Jihar Katsina zuwa iyakokin Kano, musamman a yankunan Tsanyawa, da Shanono, da Gwarzo da Karaye, tare da kira ga Gwamnatin Tarayya ta yi gaggawar ɗaukar matakan dakile barazanar ta hanyar ƙara ƙaimi wajen kare rayukan ’yan ƙasa.
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wanda shi ma shi ne Uban Jami’ar, ya yi wa ɗaliban nasiha kan su tsaya kan gaskiya da hidima ga al’umma, yana mai jaddada cewa darajar ilimi ba takardar shaidar karatu ba ce, illa tasirin da mutum zai yi a cikin al’umma.
Sarki Sanusi II, ya yaba da ci gaban da jami’ar ke samu tare da farin ciki kan yawan mata da suka kammala karatu, yana fatan hakan zai ƙara yawan rawar da mata ke takawa a mulki da sauran ɓangarorin rayuwa.
Tun da farko, Shugaban Jami’ar, Farfesa Ajith Kumar, ya bayyana cewa cikin ɗalibai 180 da suka kammala karatun 24 sun samu sakamako daraja ta ɗaya (First Class), tare da bayyana cewa wannan bikin yaye ɗaliban shi ne karo na farko da jami’ar ta raba digiri na biyu tun bayan amincewar Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), da ta samu.














