Muhammadu Sanusi II, ya bari garin Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas a gaggauce, jim kadan bayan ya gabatar da jawabinsa a babban taron tattalin arziki da zuba jari a jihar.
Sanusi yana tsakiyar gabatar da jawabinsa ne, ‘labarin LEADERSHIP’ na sake nada shi a matsayin Sarkin Kano, ya karade gari.
- Da Ɗumi-Ɗumi: An Sake Naɗa Sanusi Lamido Sanusi A Matsayin Sarkin Kano
- Da Dumi-Dumi: Majalisar Dokokin Kano Ta Rushe Masarautun Da Ganduje Ya Kirkiro
LEADERSHIP, ta bayyana cewar, an tsaurara tsaro a tattare da Sanusi lokacin da yake barin wajen taron da ke gudana a Obi Wali International Conference Center a Fatakwal, wanda hakan ya sa ‘yan jarida ba su samu damar tattaunawa da shi ba.
A halin da ake ciki, Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya taya Sanusi II murnar sake zama Sarkin Kano.
Fubara, a wata sanarwa da ya fitar a Fatakwal, ya ce ya samu labarin sake nada tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), a matsayin Sarkin Kano, wanda hakan ya sanya shi farin ciki matuka.
Gwamnan, ya kara da cewa sake nada shi sarautar da gwamnatin jihar ta yi, ya nuna cewa tsige Muhammadu Sanusi II da aka yi a ranar 9 ga watan Maris, 2020, bai yi wa al’ummar Jihar Kano dadi ba, wanda ya ce rashin adalci ne ga miliyoyin al’ummar jihar.
Ya yaba wa gwamnatin Jihar Kano bisa yadda ta saurari bukatun jama’a, tare da yin gyara kan abin da aka yi a baya, sannan ya bukaci jama’a da su bai wa Sarkin goyon baya domin samun nasara.
Fubara, ya kuma bukaci shugaban darikar Tijjanniya na Nijeriya, Muhammad Sanusi II da ya jagoranci mabiya darikar sama da miliyan 50 a Nijeriya cikin hikima da jajircewa tare da samar da zaman lafiya da adalci a tsakanin kowa a Kano.
Ya kuma yi wa Sarkin Kano na 14 fatan samun nasara tare da samar da ci gaba ga al’ummar jihar.