Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin Naira tiriliyan 3.366 na shekarar 2025.
Hakan ya biyo bayan amincewar Majalisar Dokokin Jihar Legas ta yi da kasafin a ranar Litinin.
- Jami’an Tsaro Sun Kawar Da Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Baƙo-baƙo Da Mayaƙansa A Katsina
- Sukar Gwamnatin Tinubu: Haƙiƙanin Gaskiyar Kama Obi A Abuja
Kakakin majalisar, Mudashiru Obasa, ya yaba wa ‘yan majalisar bisa ƙoƙarinsu kuma ya umarci Magatakardar Majalisar da ya aike da kasafin ga gwamnan don ya sanya hannu.
Kasafin ya ƙunshi Naira tiriliyan 1.3 don kashe kuɗaɗen yau da kullum da Naira tiriliyan 2.07 don ayyukan ci gaba.
Haka kuma, akwai giɓin Naira biliyan 408.9 wanda za a cike ta hanyar rancen kuɗaɗen daga ciki da wajen ƙasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp