Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya taya gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom da Bala Muhammad na Jihar Bauchi da Dauda Lawal Dare na Jihar Zamfara da kuma Caleb Muftwang na Jihar Filato murnar samun nasara a kotun koli.
Saraki, wanda tsohon gwamnan Jihar Kwara ne, ya bayyana cewar wannan nasara da gwamnonin suka samu nasara ce ga dimokuradiyyar Nijeriya.
- Shari’ar Kano: Kanawa Na Farin Ciki Kan Nasarar Abba A Kotun Koli
- Kotun Koli Ta Tabbatar Da Bala Mohammed A Matsayin Gwamnan Bauchi
“Ina mika sakon taya murna ga Umo Eno da Bala Mohammed da Dauda Lawal da kuma Caleb Muftwang sakamakon nasarar da suka samu a kotun koli.
“Tabbatar da su da kotu ta yi ya nuna cewa ana bin tsarin dimokuradiyya a kasarmu.”
Saraki, ya ce yana mai tabbatar musu da goyon bayansa wajen ci gaba da ayyukan alheri ga al’ummarsu.
A yau ne dai kotun koli ta yanke hukuncin karar da aka shigar a gabanta na zubukan gwamnonin da aka yi a shekarar da ta gabata.