Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano na 15, ya koma wata fada a tsohuwar garin Kano. Wannan mataki ya biyo bayan komawarsa Kano da sanyin safiyar yau Asabar, a daidai lokacin da ake ta takun-saka tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya tsige shi.
Abba Kabir Yusuf dai ya rattaba hannu ne kan dokar da ta sauke Sarki da ragowar Sarakunan da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya naɗa, inda ya ba su sa’o’i 48 da su bar fadarsu tare da miƙa su ga kwamishinan kananan hukumomi.
- Zan Gaggauta Rattaba Hannu A Hukuncin Wanda Ya Kone Mutane A Masallaci – Gwamnan Kano
- Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero
Tun a ranar Juma’a ne Gwamna Yusuf ya mayar da Muhammadu Sanusi II, kan mukaminsa, wanda Ganduje ya tsige shi a shekarar 2020. Sanusi ya karɓi wasikar sake naɗin shi ranar Juma’a kuma ya jagoranci sallar Juma’a a gidan gwamnatin Kano.
Bayan dawowarsa Aminu Ado Bayero ya samu tarba daga ɗimbin magoya bayansa, daga bisani kuma ya koma karamar fadar Nassarawa, lamarin da ya kara haifar da ruɗani. A halin yanzu, Sarki Sanusi II ya karɓe iko da fadar Gidan Rumfa.
Yanzu haka dai ana cikin tsauraran matakan tsaro a duk fadin fadar. Gwamna Yusuf ya kuma bayar da umarnin a kamo Ado Bayero, bisa zarginsa da haifar da tashin hankali a jihar.