Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya sanar da soke gudanar da bikin Hawan Sallar Layya na bana a faɗin masarautar Kano. Ya bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da zaman lafiya da kuma ba da damar gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali da natsuwa.
Sarkin ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar da yammacin Alhamis a fadarsa da ke ƙ wareofar Kudu. Ya ce an yanke shawarar ne bayan tattaunawa tsakanin Masarautar Kano da Gwamnatin Jihar Kano. Ya kara da cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne kare zaman lafiya da jin dadin jama’a.
- Saƙon Barka Da Sallah: Tinubu Ya Baiyana Tabbacin Ci Gaban Nijeriya, Da Sauyin Tattalin Arziƙi
- Bikin Sallah Babba Tare Da Malta Guinness A Kano
A baya dai, Sarkin ya umarci dukkan hakimai da su hallara a fadar Kano domin shirin hawan Sallah. Amma sai Rundunar Ƴansandan Jihar Kano ta sake tunatar da jama’a game da dokar haramta gudanar da hawan durbar a jihar, saboda matsalolin tsaro da ake fuskanta.
Sarkin ya kuma buƙaci jama’a da su yi kokarin halartar sallar Idi da kuma sallar Jumu’a, yana mai cewa akwai ladan lada mai tarin yawa ga wanda ya halarta. Ya gargadi jama’a da kada su dogara da ra’ayoyin addini da ke cewa ba dole a yi sallar Jumu’a ba idan an riga an yi sallar Idi.
A ƙarshe, ya bayyana cewa ba za a ɗauki halartar Idi a matsayin uzuri na barin Sallar Jumu’a ba, yana mai jan hankalin al’umma kan muhimmancin kiyaye dokokin addini da kuma bin tafarkin zaman lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp