Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, a ranar Talata ya yaba wa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano bisa bayar da fifiko akan ilimi, kiwon lafiya, noma, da tsaro a jihar.
Sarki Sanusi II ya bayyana jin dadinsa ne a lokacin da ya kai gaisuwar Sallah ga gwamnan Kano, kamar yadda aka saba gudanarwa a al’adance duk shekara.
- Sin Da Zambiya Sun Daddale Yarjejeniyar Fitar Da Kwarurun Macadamia Nuts
- Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi Sakamakon Rikicin Dangote Da NNPCL
“Mun zo ne domin mika gaisuwar mu ta barka da Sallah tare da gode muku bisa gagarumin aikin da kuke yi, musamman a fannin ilimi da noma, inda kuka samar da tallafin kayan aikin noma na zamani.
“Muna godiya ga Allah da ya ba mu damar shaida wannan lokaci na musamman, inda muke taruwa don sake gaishe da Gwamna a yayin bikin Sallah,” in ji shi.
Sanusi ya yabawa ‘yan majalisar dokokin jihar Kano bisa bin doka da oda da suka yi, wanda ya ce ya dawo da tsari da kimar masarautar.
“Muna fatan gwamnan zai ci gaba da yin aiki mai kyau, kuma muna kira ga shugabannin kananan hukumomin da su yi koyi da shi, su kara kaimi,” in ji Sarkin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp