Masarautar Gaya a Jihar Kano ta naɗa Alhaji Munzir Yusuf Ali a matsayin sabon Sarkin Malamai Gaya, inda za a gudanar da bikin naɗin a ranar Juma’a mai zuwa.
An naɗa shi ne biyo bayan rasuwar mahaifinsa Sheikh (Dr) Yusuf Ali, fitaccen malamin addinin Musulunci a Nijeriya watanni shida da suka gabata, wanda shi ne mai riƙe da sarautar kafin rasuwarsa.
Takardar naɗin mai ɗauke da kwanan watan 8 ga Mayu, 2024 wadda Wamban Gaya, Alhaji Mansur Ibrahim Gaya ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai, na sanar da sabon Sarkin Malaman Gaya, Alhaji Munzir Yusuf Ali ranar da za a yi taron bikin naɗa sa sarautar kamar yadda Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji (Dr.) Aliyu Ibrahim Gaya ya umurta.
Sanarwar ta hakaito cewa za a yi bikin naɗin ne a ranar Juma’a 17 ga watan Mayu, 2024 da misalin ƙarfe 10 na safe a Fadar Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji (Dr.) Aliyu Ibrahim Gaya.
Masarautar ta kuma shawarci sabon Sarkin Malaman na Gaya da ya ci gaba da shirye-shirye don tabbatar da nasarar naɗin nasa tare da yi masa addu’ar fatan alheri da nufin Allah Ya yi masa jagoranci a wannan muƙami.