• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sarkin Kano Ya Shawarci Ministan Sadarwa Kan Amfani Da Fasaha

by Khalid Idris Doya
2 years ago
Kano

Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya ce tilas ne Ministan Sadarwa, Bosun Tijani, ya tabbatar ana amfani da fasahar zamani da kuma kwarewarsa wajen yakar kalubalen tsaro a Nijeriya.

Sarki Aminu Ado Bayero wanda ya karbi bakuncin ministan a fadarsa a kwanakin bay, ya bayyana cewa minisan na da babban rawan da zai taka a yaki da matsalar tsaro, musamman a wannan yanayi da ’yan bindiga suka hana al’umma sakat.

  • Atiku Ya Ziyarci Sanata Ningi, Ya Bukaci Majalisa Kar Ta Amince Da Zalunci
  • Fara Aikin Matatar Dangote Da Ta Fatakwal: Jama’a Na Dokin Karyewar Farashin Fetur

“Da wayoyi ’yan bindiga da suke amfnai su yi magana da iyalan wadanda mutanen da suka sace, saboda haka akwai gagarumar gudummawar da ya kamata ma’aikatarka ta bayar wajen amfani da fasaha domin kamo su a hukunta su.

“Akwai bukatar ku yi amfani da fasahar zamani yadda ya kamata wajen yakar matsalar tsaro da ke kara tsanani a kasar nan, kuma mun san shugaban kasa yana da kwarin gwiwa a kanka shi ya sa ya ba ka wannan matsayi.”

“Mu kuma a bangarenmu za mu ci gaba da yi maka addu’a domin samun nasara a wannan aiki,” in ji sarkin ga minstan wanda ya je Kano domin halartar Babban Taron Majalisar Sadarwa, Kirkira da Tattalin Azikin Zamani ta Kasa (NCCIDE) karo na 11.

LABARAI MASU NASABA

Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai

Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)

Da yake mayar da jawabi, ministan ya ba wa Sarkin Kano da al’ummar Nijeriya tabbacin cewa zai yi iya kokarinsa wajen sauke duk nauyin da ya rataya a wuyansa.

“Da yardar Allah ba za mu yi kasa a gwiwa ba, wajen sauke wannan nauyi na al’umma da aka dora mana,” in ji ministan wanda ya samu rakiyarn manyan jami’an hukumomin da ke karkashin ma’aikatarsa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai
Da ɗumi-ɗuminsa

Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai

September 5, 2025
Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Wayar Da Kai Kan Barazanar Intanet A Rayuwar Al’umma (CYBER AWARENESS)

April 19, 2025
Kariya Daga Soyayyar ‘Online’ Da Shagalta A Intanet
Kimiyya Da Fasahar Sadarwa

Kariya Daga Soyayyar ‘Online’ Da Shagalta A Intanet

March 8, 2025
Next Post
Yahaya Bello Ya Ba Ma’aikata Hutu Saboda Buhari Zai Kai Ziyar Bude Wasu Ayyuka A Jihar Kogi

Zargin Badakala: Tataburzar EFCC Da Yahaya Bello Na Daukar Sabon Salo

LABARAI MASU NASABA

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

November 6, 2025
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato

November 6, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025

November 6, 2025
Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.