Sarkin Yarbawan Funtuwa wanda kuma har ila yau shi ne Shugaban kungiyar Sarakuna da Obas na Jihohin Arewa 19,Alhaji Murtala Adeleke yayi kira da a rika sa ido sosai akan wadanda suke bada bayanan mutane ga ‘yanta’adda wadanda idan ba domin hakan ba, lamarin tabarbarewar tsaro ba zai kai ga lalacewa.
Sarkin ya yi wannan kiran ne lokacin ya yi hira da Wakilin LEADERSHIP HAUSA,in da yai bayanin babbar matsalar lamarin ta’addanci ai, duk basu wuce masu basu bayanai ba.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matafiya Da Dama A Hanyar Gusau Zuwa Funtua
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Babbar Hanyar Gusau-Funtua
Yace muddin ba a gama da su wadanda suke ba ‘yan ta’addar bayanan mutane ba,ai wannan ba ayi komai ba,saboda ai su suna tare da mutanen,duk kuma wani halin da ake ciki su suke masu bayani, domin su ‘yan ta’addarai ba su da wasu bayaan mutane irin halin da suke ciki, sai ta hanyar.
Shugaban kungiyar ya jinjinawa kokarin da gwamnoni su keyi na Jihohin, Arewa19 dangane da matsalar tsaro da ake fuskanta wadda kuma ta zama ruwan dare game duniya,ya kara bayanin“Ko shakka babu,suna iyakar kokarinsu na kawo karshen ta’addanci da kuma garkuwa, da al’umma, amma duk hakar tasu ba zata iya cimma ruwa ba,har sai idan suna samun hadin kan mutane wadanda suke zama garuruwansu wajen bada bayanin ko zakulo duk wanda aka san mai kai ma ‘yan ta’adda bayanai ne”
Aikin bayyana informer,wato mai,ko masu bada bayanin halin da ake cikin,idan da ace basu bada gudunmawa wajen fadawa su,‘yan ta’addar,ai da an dade da kawo karshen lamarin da ya kasancewa al’umma wani alakakai musamman ta bangaren tafiyarda rayuwa.Bugu da kari ma, ko maciji aka kashe idan ba’a samu damar sare kan ba,to da akwai babbar matsala, haka ne lamarin yake, idan ana kashe ‘yan ta’adda amma,ta bangaren daya kuma ga masu aika masu da bayanai nan suna ta yawonsu a cikin gari, ai tamkar da Karin maganar nan da Hausawa ke yi ta“Ba ‘a rabu da Bukar bane, sai gas hi an haifi Habu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp