Wasu alkaluma na ma’aikatar raya masana’antu da fasahar sadarwar kasar Sin, sun nuna yadda sashen kera batiran lithium na kasar ya samu ci gaba da kaso 25 bisa dari a shekarar 2023 da ta gabata.
Alkaluman sun nuna yadda jimillar karfin batiran da aka sarrafa a kasar a baran, ya kai sa’o’in gigawatt 940. Adadin da darajarsa ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 1.4, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 197. (Saminu Alhassan)