Sashen masana’antun kirar motoci na kasar Sin, ya samu ci gaba ta fuskar kera motoci da sayar da su a watan Yulin bana. Alkaluman da kungiyar makera motoci ta kasar Sin ko CAAM ta fitar a Litinin din nan sun nuna cewa, a watan na Yuli, sashen ya fitar da adadin motoci miliyan 2.591, adadin da ya karu da kaso 13.3 bisa dari a mizanin shekara, yayin da fannin sayar da motocin ya samu karuwar kaso 14.7 bisa dari, inda aka fitar da adadin da ya kai miliyan 2.593.
Kazalika, adadin motocin da sashen masana’antun ya samar cikin watanni bakwai na shekarar ta 2025 ya karu da kaso 12.7 bisa dari zuwa adadin motoci miliyan 18.24, yayin da adadin wadanda aka sayar ya karu da kaso 12 bisa dari wato adadin motoci miliyan 18.27. (Saminu Alhassan)













